Coronavirus: Mun zafafa daukar matakai —Ganduje

Gwamnatin Kano ta ce ta dauki matakan kandagarki don dakile yaduwar cutar coronavirus bayan da aka samu mutum na farko mai dauke da ita a jihar. Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana haka a wani jawabi da ya yi wa al’ummar jihar ranar Asabar. A cikin matakan, inji gwamnan, an umarci matuka keke mai […]

Coronavirus: Mun zafafa daukar matakai —Ganduje

Gwamnatin Jihar Kano ta ce an yi feshin ne a masallatai da majami’u da kasuwanni 31

Gwamnatin Kano ta ce ta dauki matakan kandagarki don dakile yaduwar cutar coronavirus bayan da aka samu mutum na farko mai dauke da ita a jihar.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana haka a wani jawabi da ya yi wa al’ummar jihar ranar Asabar.

A cikin matakan, inji gwamnan, an umarci matuka keke mai kafa uku, wanda aka fi sani da “A Daidaita Sahu” a jihar, da kada su dauki fasinja fiye da daya a lokaci guda.

Gwamnan ya tabbatar da cewa wanda aka samu da cutar wani tsohon ma’aikacin diflomasiyya ne wanda bai yi tafiye-tafiye zuwa kasashen waje ba a watanni shida da suka gabata.

“Mun tabbatar da cewa gwaji ya nuna wani ma’aikacin diflomasiyya mai shekara 75 da haihuwa da ya yi ritaya ya kamu da cutar. Wannan ne mutum na farko a Kano”, inji Dokta Ganduje, wanda ya kara da cewa, “Yanzu haka mutumin yana samun kulawa a cibiyar killace masu dauke da cutar da ke Kwanar Dawaki, kuma tuni muka binciko mutanen da suka yi mu’amala da shi”.

Gwamnan ya kara da cewa, “An ce mutumin ya je Legas da Abuja da Kaduna a makwanni biyu da suka wuce, kuma ranar 25 ga watan Maris ya dawo daga Kaduna”.

Kamfanin Dillacin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito gwamnan yana jaddada cewa za a bukaci karin hadin kan malaman addini da shugabannin ’yan kasuwa don ganin an ilmantar da mutane game da matakan da ya kamata a dauka don hana cutar yaduwa.

Gwamnatin jihar Kano na cikin wadanda suka fara daukar matakan hana shigar cutar ta hanyar rufe iyakokinsu.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno