Coronavirus: Mutum 154,225 sun warke a Najeriya
Har yanzu akwai mutum 7,599 masu dauke da kwayoyin cutar a fadin Najeriya.
Hukumar dakile cututtuka masu yaduwa a Najeriya NCDC, ta bayar da tabbaci kan warkewar mutum 154,225 daga cutar Coronavirus a kasar tun bayan bullarta a shekarar da ta gabata.
Hakan na kunshe ne cikin alkaluman da hukumar ta fitar kan shafinta na Twitter a ranar Talata.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa, daga ranar 4 zuwa 10 ga watan Afrilun da muke ciki, an samu mutum 1,661 da suka warke daga cutar.
Sai dai alkaluman da NCDC ta fitar sun nuna cewa har yanzu akwai mutum 7,599 masu dauke da kwayoyin cutar a fadin Najeriya.
Haka kuma, NCDC ta ce an samu karin mutum 74 sabbin kamuwa da cutar cikin sa’a 24 da ta gabata, jimillar da ta kai adadin wadanda cutar ta harba a fadin kasar zuwa 163,911.
Daga cikin jihohi da aka samun karin sabbin kamuwa Legas na da mutum 30, sai kuma Enugu mai mutum 11 da kuma Abuja ita ma da mutum 11.
Sauran jihohin da aka samu wanda cutar ta harba sun hada da Akwa Ibom mai mutum 8, Osun da mutum 5, hudu a Kaduna, sai biyu a Ebonyi.
Kazalika, an samu mutum biyu a Ribas da kuma mutum daya a Ekiti.
Ya zuwa yanzu dai mutum 1,803,177 aka yi wa gwajin cutar tun bayan sanar da bullarta karon farko a ranar 27 ga watan Fabrairun 2020.