Mutum 245 sun warke daga coronavirus a Abuja
An sallami karin mutum 30 da suka warke daga cutar coronavirus a Babban Birnin Tarayya Abuja. Minista Mohammed Musa Bello, ta shafinsa na Twitter ya ce yanzu mutum 245 ne suka warke daga cutar ta coronavirus a birnin . “Ina muku albishir cewa an sallami karin mutum 30 da suka warke daga cibiyar killace masu […]
An sallami karin mutum 30 da suka warke daga cutar coronavirus a Babban Birnin Tarayya Abuja.
Minista Mohammed Musa Bello, ta shafinsa na Twitter ya ce yanzu mutum 245 ne suka warke daga cutar ta coronavirus a birnin .
“Ina muku albishir cewa an sallami karin mutum 30 da suka warke daga cibiyar killace masu cutar COVID-19 a Abuja.
“Yanzu an sallami mutum 245 ke nan a Yankin Birnin Tarayya”.
Dear FCT residents,
I bring you good news as we successfully treated and discharged additional thirty (30) #COVID19 patients from our treatment facilities in the FCT.
The total number of discharged patients in the FCT is now 245. #StaySafe #TakeResponsibility
— Mal. Muhd Musa Bello (@MuhdMusaBello) June 6, 2020
Ministan ya kuma bukaci mazauna birnin da su rika kula da lafiyarsu da kuma matakan kariya daga cutar.
Ya ce abun da ya fi dacewa shi ne bin shawarwarin hukumomin lafiya da kula da matakan kare kai daga kamuwa.
Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa (NCDC) ta ce mutum 862 suka harbu tun bayan bullar cutar COVID-19 a Abuja.
Daga cikin adadin mutum 22 sun rasu baya ga 245 da aka sallama zuwa yanzu.