Coronavirus: Na fidda ran zan rayu –Dan Najeriya mazaunin Amurka

Alhaji Ibrahim Garba dan Najeriya ne da ke zama a birnin New York na Amurka, wanda kwanan nan aka sallame shi daga asibiti bayan ya yi fama cutar Coronavirus. A tattaunawarsa da Aminiya ta waya ya yi bayyana yadda ya tsallake rijiya da baya, bayan ya yi fama da jinyar cutar a asibiti na tsawon […]

Coronavirus: Na fidda ran zan rayu –Dan Najeriya mazaunin Amurka

Alhaji Ibrahim Garba

Alhaji Ibrahim Garba dan Najeriya ne da ke zama a birnin New York na Amurka, wanda kwanan nan aka sallame shi daga asibiti bayan ya yi fama cutar Coronavirus. A tattaunawarsa da Aminiya ta waya ya yi bayyana yadda ya tsallake rijiya da baya, bayan ya yi fama da jinyar cutar a asibiti na tsawon kwana 16:

Yaya ka ji lokacin da ka fahimci ka kamu da cutar Coronavirus?

Lallai lamarin akwai abin tashin hankali sosai yadda na tsinci kaina a dakin gobe-da-nisa. Lokacin da na farfado bayan sa’o’i 24 sai likitoci suka zo suka fada mini cewa; shin ko ka san shahararriyar cutar nan ta Coronavirus?

To wane amsa ka ba su?

Na ce eh, na sani. To sai  suka ce mini ai ina da cutar sarkewar numfashi na nimoniya (pneumonia) wadda ita ce ma babbar matsalar kuma ina fama da Coronavirus. Na yi ta tunanin cewa rayuwata ta zo karshe ke nan, domin ina jin ba ni da sauran shan ruwa a gaba. Don haka sai na yawaita yin salati. To amma sa’o’i kadan bayan nan sai aka fada min cewa za a ci gaba da rike ni a asibitin inda wadansu mutane da suka yi fama da makamanciyar larurar da nake fama da ita aka sallame su daga bisani.

Bayan kwana 10 ana ta yi mini magani sai na samu damar farfadowa, sai likitana ya tabbatar min cewa na kamu da cutar Coronavirus sai dai ya ce za ka samu sauki nan ba da jimawa ba.

Yaya sunan asibitin da aka kwantar da kai a New York, kuma tun yaushe aka kwantar da kai da ranar da aka sallame ka?

Sunan asibitin Saint Barnabas Hospital Brond, a New York. An kwantar da ni a ranar 30 ga Maris sannan an sallame ni ranar 15 ga Afrilu.

Ko za ka fada mana kudin da ka kashe a asibiti kafin ka samu lafiya?

Ban biya ko sisi ba,  kuma ba wanda ya ce mini in biya ko kwandala. Sai dai kawai an ce mini in rika tuntubar likitana a-kai-a- kai idan ina da bukatar a rubuta mini wasu magunguna, kuma suna kirana kullum domin jin halin da nake ciki.

An ce kamar ka fara yi wa kanka magani tun daga gida. Wadanne magunguna ne kuma ko sun yi tasiri?

Eh, lokacin da na fara jin alamun zazzabi sai na fara yin surace; ina shan citta da tafarnuwa da sauran jike-jiken maganin gargajiya.

Wadanne alamu ka fara ji, kafin cutar ta fara tasiri a kanka? Na fara jin ciwon kai mai tsanani da zazzabi mai zafin gaske. Ina kuma yawan yin tari tare da jin sarkewar majina a kirji wanda ba ta iya fita. Amma mafi munin cikinsu shi ne bushewar makwagoro hade da matsanancin kishiruwa wanda idan ma ka sha ruwan sai ya kara munin abin. Saboda da zarar ka sha ruwan sai ka ji tamkar ana gurza maka kaca a makwagoron.

Ko a ina kake jin cewa ka dauko kwayar cutar?

Gaskiya wannan tambayar tana da tsauri. Sai dai na halarci wani taron daurin aure a Tsibirin Staten da ke nan Amurka inda muka ji cewa akwai wata da ta halarci bikin kuma ta rasu, sai kuma muka sake jin wani ma da ya halarci bikin shi ma ya rasu.

To da na fara jin wadansu sun kamu da cutar kuma sun rasu wadansu kuma suna fama da ita daga nan sai na fara jin cewa ya kamata in killace kaina; inda na yi hakan na tsawon mako uku: amma ina lamarin sai ya ta’azzara. Kawai ina ganin lallai a wajen bikin ne na kamu da cutar saboda wadansu sun yi ta rashin lafiya inda wadansu daga ciki suka warke wadansu kuma suka rasu. Don haka ina da yakinin cewa daga can na harbu da cutar.

Don haka kana ganin bayar da tazara shi ne muhimmin matakin kauce wa kamuwa da cutar ke nan?

Haka ne a gaskiya. Ai kamar kana musabaha ne da babban abokinka da kyakkyawar niyya ko kuma ka karbi wani abu daga wajensa kuma bai san cewa yana dauke da ita ba. To daga nan matsalar take samo asali. Kawai babbar hanyar yaki da yaduwar cutar ita ce a rika yin tazara da juna ko ta halin kaka.

Wane irin radadin ka samu kanka ciki yayin jinyar cutar?

Wani irin radadi ne marar misaltuwa wanda sai dai kawai mutum ya ji shi kwakwalwalsa kuma ina mamakin ko ta yaya zan iya jure wa irin wannan radadi. Za ka ji bushewa na gaske a makoshinka wanda shan ruwa ba zai iya sanyaya shi ba. Za ka ji kamar ana kartar farce da kuma gilashi a cikin makoshin. Za ka ji kamar ana yi maka yankan rago ne kamar mutum ba zai sake rayuwa ba. An saka mini na’urar taimaka wa numfashi. A lokacin na ji haka sai na ce shi ke nan tawa ta zo karshe kuma na fidda ran sake shan ruwa a duniya.

Yaya za ka kwatanta kwana 16 da ka yi a asibiti a birnin New York?

Kwana 10 na farko masu matukar wuyar lamari ne kuma na yi su ne cikin halin ban san ina nake ba. An yi ta saka mini magunguna daban-daban, bayan nan ne na farfado. Sai kuma na fara jure wa wahalhalun samun waraka a asibitin.

Kozakafadiirinmagungunan da aka rika yi maka?

Magungunan antibiotics da na hydroclorokuine tare da yin gwajin jini a-kai-a-kai da auna yanayin gabobin jikina da kuma gwajin x-ray da sauransu aka rika yi min-.

Yaya za ka kwatanta mace- macen da aka yi ta samu dalilin cutar a asibitin da ka kwanta?

Ba zan iya fadin komai a kai ba saboda ni ma an killace ni a waje na daban ne ni kadai kuma babu wasu bayanai da ake ba ni a matsayina na marar lafiya. Sai dai wadansu jami’an jinya (nas-nas) ke cewa wani ya rasu a layin da muke; amma kai kana da kwarin yakar cutar.

Mene ne sakonka ga ’yan Najeriya kan illar cutar?

Ya kamata su dauki lamarin cutar da muhimmanci, lura da yadda har yanzu cutar tana nan ba ta kau ba. Lokacin da cutar ta shafi kasar Italiya ba wanda ya yi tunanin za ta yi illar gaske a Amurka. Ina da fargaba sosai game da ita, mutane su ne ke da damar daukar matakan kariya daga ita. Cuta ce mai kisan mutane cikin sauki.

Rahotanni sun ce bakaken fata sun fi hallaka daga cutar  a kan fararen fatar Amurka. Kasancewar an kwantar da kai saboda kamuwa da cutar, me za ka ce kan haka?

Akwai alamun hakan musamman ma a yankin da nake zama, wanda yake waje ne da jinsin mutane daban-daban ke zaune. Amma ba zan iya tabbatar da eh ko a’a ba. Sai dai a kafofin labarai a nan ana ta yayata hakan.

Kana da kwarin gwiwar yanayin kiwon lafiyar Najeriya zai iya yaki da cutar yadda ya kamata?

Eh, a kullum ina fata harkar kiwon lafiyar Najeriya ta inganta sosai. Amma maganar gaskiya, a irin tsarin da muke ciki a yanzu a Najeriya, ban san yadda za mu iya samar da kiwon lafiya ga jama’a domin yakar wannan cuta ba.