Coronavirus: ‘Rufe kasuwanni ka iya haddasa mutuwa’

Tun bayan da hukumomi a Najeriya suka fara ayyana dokokin hana fita ko hana bude harkokin kasuwanci wasu ’yan kasa suka fara kokawa da yadda matakin ka iya shafar rayuwarsu.  Jaridar Aminiya ta tattauna kwanan baya da Farfesa Garba Ibrahim Sheka, malami a Sashen Nazarin Tattalin Arziki na Jami’ar Bayero ta Kano a kan tasirin […]

Coronavirus: ‘Rufe kasuwanni ka iya haddasa mutuwa’

Sugaban KANSIEC, Farfesa Garba Ibrahim Sheka

Tun bayan da hukumomi a Najeriya suka fara ayyana dokokin hana fita ko hana bude harkokin kasuwanci wasu ’yan kasa suka fara kokawa da yadda matakin ka iya shafar rayuwarsu.

 Jaridar Aminiya ta tattauna kwanan baya da Farfesa Garba Ibrahim Sheka, malami a Sashen Nazarin Tattalin Arziki na Jami’ar Bayero ta Kano a kan tasirin da haramta harkokin ka iya yi ta fuskar tattalin arziki.

 Mece ce barazanar da rufe kasuwanni da hanyoyi  za ta yi ga al’ummar Najeriya, saboda cutar Kurona?

Babbar barazanar da muke ciki ita ce yadda za a hana yaduwar wannan cuta a Najeriya, lura da yadda al’adunmu suke na cudanya da juna a kasuwanni da sauran al’amuran yau da kullum.

Duk lokacin da aka ce an rufe kasuwanni da wuraren sana’o’i, to wannan barazanar ita ma annoba ce mai zaman kanta, domin mutanen da za su mutu saboda yunwa suna iya fin wadanda annobar coronabirus za ta shafa domin kashi 64 cikin 100 na mutanen Jihar Kano  da sauran sassan Najeriya, sai sun fita suke samun abin da za su ci su da iyalansu.

Wadansu sai sun je sun yi dako, wadansu ruwan da za su sha kawo musu ake yi daga nesa.

Idan yau aka ce an kulle kasuwanni da hanyoyi, to, mutanen da yunwa za ta hallaka suna da yawan gaske…

 Wanne rigakafi ya kamata a yi wa tattalin arziki?

Rigakafin da za a yi wa tattalin arziki ya danganta da irin arzikin da kasa ke da shi, kuma a halin yanzu Najeriya tattalin arzikinta yana cikin halin rauni, domin sai an sayar da man fetur ake samun kudin da ake aiwatar da kasafin kudi, kasuwar mai yanzu haka ta fadi warwas!

Don haka ita kanta yanzu kasar tana fama ta matsin tattalin arziki. Ga shi kasashen da ake neman tallafinsu su ma suna fama da kansu.

Ya kamata gwamnatoci a matakai daban-daban su fito da wani tsari da zai tallafa wa ’yan kasa, domin tattalin arziki a yanzu yana cikin wani hali. Lallai wannan al’amari yana bukatar a koma ga Allah domin neman mafita. 

Ga shi muna tunkarar damina wane  tasiri wannan yanayi zai yi a kan harkar noma?

Da farko dai illar ta fi yawa a cikin birane domin ana zancen hana cinkoso ne watakila ma iya cewa idan har al’amarin bai yi kamari ba, ba zai yi wa noma illa sosai ba.

Amma fa idan aka ce an rufe kasuwanni wanda a nan ake sayo kayan aikin noma, to, gaskiya sha’anin zai yi illa wa harkar noma.

Idan aka ce ba a yi noma ba, to lallai al’amura za su kara dagulewa wanda ba ma fatar haka ta kasance.

Sannan ya kamata Gwamnatin Tarayya ta samar da karin madatsun ruwa sannan ta inganta wadanda muke da su domin tallafa wa noman rani ya kasance a kowane yanayi za a iya noma, wannan zai kara samar da aikin yi ga matasa sannan zai kara sa Najeriya ta dogara da kanta a bangaren abinci.

 Wace rawa shugabannin kananan hukumomi ya kamata su taka wajen kawo wa jama’a dauki?

Idan aka yi wa abin dubi na tsanaki, shugabannin kananan hukumomi babu wani dauki da za su iya kawo wa al’umarsu domin harka ce ta kudi, kuma kowa ya san halin da suke ciki.

Su suka fi kusa da jama’a amma babu wani abu da za su iya.

Kuma idan aka ci gaba da wannan yanayi na tsawon wata daya ko biyu to hatta kudin da ake rabawa na arzikin kasa zai yi karancin da za a shiga mummunan hali. Allah Ya kiyaye.

 Ko akwai yiwuwar shiga masassarar tattalin arziki?

A halin yanzu tattalin arzikin duniya ya shiga masassara, hatta kasar China da take da karfin tattalin arziki a duniya tana fuskantar wannan yanayi — tana amfani da kashi 30 cikin 100 na kayan da take yi tana kuma fitar da kashi 70.

To yanzu haka komai ya tsaya cik a duniya. Don haka tattalin arzikin kasashe da dama ya ruguje, kasuwanin hannayen jari sun fadi warwas  a fadin duniya, hatta a kasar Amurka da Tarayyar Turai  suna cikin wannan yanayi na fama da tattalin arzikin kasa.

Mece ce mafita ga wannan hali da ake ciki?

To idan har Allah Ya takaita wannan yanayi da muka shiga, lallai ya kamata gwamnati ta ci gaba da lalubo hanyar fadada tattalin arziki, ta mai da hankali wajen inganta masana’antu da ba su tallafi da kuma bunkasa harkar noma sannan kada Najeriya ta nace da noman shinkafa kadai idan har noman shinkafa bai karbe mu ba, to a lalubo wani nau’in hatsin da za a rika nomawa.

Domin har yanzu a Najeriya shinkafar da ake nomawa a sauran sassan duniya ta fi ta Najeriya araha, dole sai an samu hanyar da za a bi wajen kawo sauyi saboda idan aka fi ka arha, dole za a fi ka ciniki.

Sai a kyale shinkafa a dukufa noman wani hatsin da za a rika noma shi cikin sauki wanda zai kasance mai arha idan an noma shi yadda zai dace da kasuwar duniya.

Idan har sai mun kashe Naira dubu 18, za mu iya noma buhun shinkafa sannan ga wata can da aka noma a wata kasa ana iya saida ta a kan 5,000, to babu dalilin da za mu tsaya a kan wannan yanayi, dole mu hakura mu sayi mai araha idan ya so mu kuma mu duba mu ga abin da zai karbe mu. Misali kamar gyada ko wake sai a tsaya a kansu a inganta su.

A samar da dokoki da za su karfafa masana’antu da harkar noma, a ci gaba da ba da tallafi, ba lallai sai mun kai kayayyakinmu waje ba, idan muka iya samar wa kanmu abin da muke da bukata to a sannu Najeriya za ta mamaye kasuwar Afirka ta Yamma da  ta Tsakiya.

Sannan a inganta gina kasa ta hanyar samar da kayayyakin more rayuwa kamar wutar lantarki da hanyoyi da layin dogo da inganta hakar lafiya da ilimi da tsaro da sauransu.