Coronavirus ta kashe karin mutum 7 a Najeriya, 838 sun kamu

Alkaluman Hukumar Dakile Cututtuka Masu Yaduwa a Najeriya NCDC, sun nuna cewa an samu karin mutum 838 da cutar Coronavirus ta harba ranar Lahadi a fadin kasar. Cikin bayanan da hukumar ta wallafa a shafinta na yanar gizo kamar yadda ta saba duk rana sun nuna an kuma samu karin mutum bakwai da suka mutu […]

Coronavirus ta kashe karin mutum 7 a Najeriya, 838 sun kamu

Wani Jami’in kiwon lafiya daga cikin gidan gilashi yana daukar samfuri daga jikin wata mata da ake yiwa gwajin coronavirus a jihar Ogun

Alkaluman Hukumar Dakile Cututtuka Masu Yaduwa a Najeriya NCDC, sun nuna cewa an samu karin mutum 838 da cutar Coronavirus ta harba ranar Lahadi a fadin kasar.

Cikin bayanan da hukumar ta wallafa a shafinta na yanar gizo kamar yadda ta saba duk rana sun nuna an kuma samu karin mutum bakwai da suka mutu sakamakon cutar a fadin Najeriya.

Sabbin alkaluman da suka nuna an samu karin mutum 838 da suka harbu sun fito ne daga jihohi 16 da suka hada da; Abuja (297), Legas (253), Filato (82), Kaduna (57), Katsina (32), Nasarawa (31) da Kano (25).

Sauran su ne; Gombe (24), Oyo (8), Ribas (8), Zamfara (7), Ogun (4), Bauchi (4), Edo (4), Anambra (1) da kuma Sakkwato (1).

Da wannan adadi, jimillar mutum 84,414 sun harbu da cutar a Najeriya, yayin da kuma mutum 1,254 suka riga mu gidan gaskiya.

Ya zuwa yanzu dai an salami mutum 71,034 daga cibiyoyin killace masu dauke da cutar bayan sun samu waraka.