Coronavirus ta kashe mutum 9 a Najeriya, 917 sun kamu
A ranar Lahadi an samu karin mutum 9 da suka mutu a Najeriya sakamakon cutar Coronavirus a yayin da aka samu mutum 917 sabbin kamuwa. Hakan na kunshe ne cikin kididdigar alkaluman da Hukumar Dakile Cututtuka Masu Yaduwa a Kasa NCDC ta fitar kamar yadda ta saba duk rana. An umarci Ma’aikatan Legas su ci […]
A ranar Lahadi an samu karin mutum 9 da suka mutu a Najeriya sakamakon cutar Coronavirus a yayin da aka samu mutum 917 sabbin kamuwa.
Hakan na kunshe ne cikin kididdigar alkaluman da Hukumar Dakile Cututtuka Masu Yaduwa a Kasa NCDC ta fitar kamar yadda ta saba duk rana.
- An umarci Ma’aikatan Legas su ci gaba da aiki daga gida saboda Coronavirus
- Sabon albashi: Za a koma biyan N30,000 a Gombe
- ’Yan sanda sun watsa casun tsiraici a Adamawa
Alkaluman sun nuna an samu karin mutum 222 da suka kamu a Abuja, sai mutum 214 a Jihar Legas da kuma karin mutum 92 a Jihar Filato.
A Jihar Nasarawa an samu mutum 50, sai Oyo mai mutum 41 da kuma Adamawa mai mutum 33 yayin da aka samu mutum 32 a Ondo.
Cikin sa’a 24 an samu karin mutum mutum 28 a Abiya, da mutum 19 a Ogun sai mutum 17 da suka harbu a Jihar Ribas.
Jihar Kano ta samu karin mutum 16, sai Yobe na da mutum 14 da kuma mutum 8 a Edo, sai Anambra mai mutum 6 yayin da kuma aka samu karin mutum 5 a Ekiti da kuma mutum daya a Jigawa.
A jimillance yanzu cutar Coronavirus ta harbi mutum 90,080 a fadin kasar tun bayan bullarta karon farko a watan Fabrairun 2020.
Kazalila, alkaluman na NCDC sun nuna cewa cutar ta kashe adadin mutum 1,311 yayin da tuni an salami mutum 75,044 bayan samun waraka.