Coronavirus ta kashe Shugaban Hukumar Kwallon Kafar Akwa Ibom

Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya (NFF) ce ta sanar da rasuwarsa a ranar Talata.

Coronavirus ta kashe Shugaban Hukumar Kwallon Kafar Akwa Ibom

Emmanuel Ibah, Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Akwa Ibom

Emmanuel Ibah mai shekaru 61, wanda mamba ne a Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya (NFF) mai wakiltar Kudu maso Kudu ya rasu a sakamakon kamuwa da cutar coronavirus.

An sanar da rasuwar tasa ce a ranar Talata, kamar yadda Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya ta sanar.

“Iyalai sun sanar da NFF rasuwar Ibah bayan kamuwarsa da cutar COVID-19.

“Kafin rasuwarsa ya kasance yana fama da ciwon suga da hawan jini,” kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Mamacin ya samu mukami a ne NFF a ranar 18 ga watan Satumbar 2018.

Bayan sake bullar cutar COVID-19 a karo na biyu, mutane da dama sun kamu da ita baya ga wadanda suka rasa rayukansu a sanadiyyarta.