Coronavirus ta sake kashe karin mutum 11 a Najeriya

Mutum 11 ne suka mutu ranar Juma’a a fadin Najeriya sakamakon kamuwa da cutar Coronavirus, lamarin da ya kawo jimillar adadinsu zuwa 1,212. Hakan na kunshe ne cikin kididdigar alkaluman da Hukumar Dakile Cututtuka Masu Yaduwa a Najeriya NCDC ta fitar a daren jiya na Juma’a, 18 ga watan Disambar 2020. Ce-ce-ku-ce kan wanda ya […]

Coronavirus ta sake kashe karin mutum 11 a Najeriya

Shugaban Hukumar NCDC; Chukwemeka Ihekweazu

Mutum 11 ne suka mutu ranar Juma’a a fadin Najeriya sakamakon kamuwa da cutar Coronavirus, lamarin da ya kawo jimillar adadinsu zuwa 1,212.

Hakan na kunshe ne cikin kididdigar alkaluman da Hukumar Dakile Cututtuka Masu Yaduwa a Najeriya NCDC ta fitar a daren jiya na Juma’a, 18 ga watan Disambar 2020.

Alkaluman na NCDC sun nuna an samu karin sabbin mutane 806 da cutar ta harba a birnin Abuja da wasu jihohi 25 daga cikin 36 daga fadin kasar.

Sabbin mutane 806 da cutar ta harba daga jihohi 26 sun kasance kamar haka: Legas (287), Abuja (255), Kaduna (36), Akwa Ibom (29), Katsina (25), Ribas (25), Kwara (21), Bauchi (19) da Kano (15).

Sauran su ne; Ondo (14), Filato (13), Yobe (12), Nasarawa (11), Ebonyi (9), Gombe (8), Abiya (7), Delta (4), Imo (4), Osun (3), Anambra (2), Borno (2), Kuros Riba (1), Edo (1), Ekiti (1), Jigawa (1), da Ogun (1)

A yayin da likafar cutar ta ke sake ci gaba babu sassauci, har yanzu jihar Legas ce ke jan ragama ta yawan masu cutar inda ta harbi mutum 26,182, sai kuma mutum 23,898 da suka warke, yayin da mutum 234 suka kwanta dama a jihar.

Kawo yanzu a duk fadin Najeriya, cutar ta harbi mutum 77,013 sai kuma mutum 67,484 da aka sallama daga cibiyoyin killace masu cutar bayan sun samu waraka.

Taskar bayanai ta NCDC ta nuna cewa, an yi wa mutum 869,362 gwajin cutar a duk fadin kasar tun bayan bullarta karo na farko a watan Fabrairun bana.

Haka kuma alkaluman Cibiyar dakile cututtuka ta kasar sun nuna cewa, mutum 8,317 ne suka rage masu dauke da kwayoyin cutar.