Coronavirus ta yi ajalin wani tsohon dan Majalisar Kano

Tsohon dan majalisa da ya wakilci Jihar Kano a Tarayya tun a jamhuriyya ta biyu, Dokta Abdullahi Maikano Rabi’u, ya riga mu gidan gaskiya bayan shafe shekara 72 a ban kasa. Tsohon mashawarci na musamman ga tsohon gwamnan Jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau a kan harkokin da suka shafi tattalin arziki ya rasu ne a […]

Coronavirus ta yi ajalin wani tsohon dan Majalisar Kano

Jihar Kano a taswira

Tsohon dan majalisa da ya wakilci Jihar Kano a Tarayya tun a jamhuriyya ta biyu, Dokta Abdullahi Maikano Rabi’u, ya riga mu gidan gaskiya bayan shafe shekara 72 a ban kasa.

Tsohon mashawarci na musamman ga tsohon gwamnan Jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau a kan harkokin da suka shafi tattalin arziki ya rasu ne a sakamakon bayan ya yi fama da cutar Coronavirus.

Marigayi Maikano wanda kwararren likitan dabbobi ne ya rasu ne a cibiyar killace masu cutar Coronavirus da ke Kwanar Dawaki a Jihar.

Ya rasu ya bar matarsa daya da ’ya’ya da kuma jikoki da dama.

Alhaji Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya inganta rahoton mutuwar wanda ya kasance daya daga cikin manyan abokai ga mamacin.

Ya ce mamacin ya taba rike mukamin mataimakin babban Manaja a tsohon Bankin Arewa da kuma shugaba a Bankin Kasuwanci na Kano.

Har ya zuwa lokaci da mai yankan kauna ta katse masa hanzari, Dokta Maikano shi ne mai rike da mukamin Dallatun Bichi kuma Dagacin garin Dawakin Tofa.