Coronavirus: Wadanda suka kamu sun kai 238
A yanzu yawan wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar coronavirus a Najeriya ya kai 238. Adadin ya kai haka ne bayan da Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta bayar da sanarwa cewa an tabbatar da samun sabbin kamuwa mutum shida. “Zuwa karfe 9.30 na daren 6 ga watan Afrilu, akwai […]
A yanzu yawan wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar coronavirus a Najeriya ya kai 238.
Adadin ya kai haka ne bayan da Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta bayar da sanarwa cewa an tabbatar da samun sabbin kamuwa mutum shida.
“Zuwa karfe 9.30 na daren 6 ga watan Afrilu, akwai mutane 238 da aka tabbatar sun kamu da COVID-19 a Najeriya. An sallami 35 daga cikinsu, yayin da mutum biyar suka rasu”, inji NCDC a sanarwar da ta wallafa a shafinta na Twitter.
Biyu daga cikin sababbin kamuwar dai a jihar Kwara suke, biyu a jihar Edo, daya a jihar Ribas, daya a Yankin Babban Birnin Tarayya.
Ministan Lafiya Osagie Ehanire ya ce gwamnati ta kuduri aniyar kara yawan wadanda ake yiwa gwaji da killace wadanda ake tunanin sun kamu da wuri, da kuma inganta hanyoyin bibiyar wadanda suka yi mu’amala da wadanda aka tabbatar sun kamu.