Coronavirus: ’Yar wasan kwaikwayo za ta biya tara

An umarci wata shaharariyar ’yar wasan kwaikwayon nan ta masana’antar fina-finai ta Nollywood mai suna Funke Akindele, wacce aka fi sani da Jenifa da mijinta Abdulrashid Bello su biya tarar N100,000 ko wannensu bayan da aka same su da laifin saba dokar hana taro domin kauce wa yada coronavirus. Wata kotun majistare da ke Ogba […]

Coronavirus: ’Yar wasan kwaikwayo za ta biya tara

Funke Akundele-Bello da mijinta sun saba doka ne saboda sun tara mutum fiye da 20

An umarci wata shaharariyar ’yar wasan kwaikwayon nan ta masana’antar fina-finai ta Nollywood mai suna Funke Akindele, wacce aka fi sani da Jenifa da mijinta Abdulrashid Bello su biya tarar N100,000 ko wannensu bayan da aka same su da laifin saba dokar hana taro domin kauce wa yada coronavirus.

Wata kotun majistare da ke Ogba ce ta yanke wannan hukuncin ranar Litinin 6 ga watan Afrilu bayan da suka amsa laifin da aka tuhume su da shi, sannan ta wajabta masu aikin sa-kai na kwana 14.

Ma’auratan dai sun amsa laifin da ake tuhumar su da aikatawa na shirya wani kwarya-kwaryan bikin taya Bello, wanda aka fi sani da JJC Skillz murnar zagayowar ranar haihuwarsa ranar Asabar a cikin gidansu da ke Lekki a Legas, lamarin da ya yi karan tsaye ga dokar gwamnati ta hana taron mutane da dama.

Antoni janar kuma kwamishinan shari’a na jihar Legas Moyosore Onigbanjo (SAN) ne ya gabatar da masu laifin a gaban kotun.

Tun da farko dai kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Legas Bala Elkana ya ce an jawo hankalin jami’an tsaro ne ga wani bidiyo da ke yawo a kafofin sadarwa na zamani inda mutane masu dimbin yawa wadanda galibinsu shahararrun ‘yan wasan kwaikwayo ne da mawaka ke halarta wani biki.

“Nan take aka tura ‘yan sanda suka kamo Funke Akindele. Ana ci gaba da bincike kuma an matsa kaimi don ganin an kamo sauran mutanen da ke cikin bidiyon wadanda suka hada da Azeez Fashola, wanda aka fi sani da Naira Marley”, inji Elkana.

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50