Coronavirus: Yawan wadanda suka kamu ya kai 174
A karo na biyu a ranar Laraba hukumomin lafiya a Najeriya sun tabbatar da samun karin mutunen da suka kamu da cutar coronavirus. Sababbin alkaluman dai sun nuna cewa an samu karin mutum 23; abin da ya kai adadin wadanda aka tabbatar a Larabar kadai zuwa 35. Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa (NCDC) ta […]
A karo na biyu a ranar Laraba hukumomin lafiya a Najeriya sun tabbatar da samun karin mutunen da suka kamu da cutar coronavirus.
Sababbin alkaluman dai sun nuna cewa an samu karin mutum 23; abin da ya kai adadin wadanda aka tabbatar a Larabar kadai zuwa 35.
Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa (NCDC) ta bayyana cewa a yanzu yawan wadanda aka tabbatar sun kamu ya haura 170.
“Zuwa karfe 8.00 na daren 1 ga watan Afrilu, an samu mutum 174 da aka tabbatar sun kamu da COVID-19.
“Daga cikin wannan adadi an sallami mutum tara, yayin wasu mutum biyu suka riga mu gidan gaskiya”, inji NCDC.
Abba Kyari na murmurewa —Kwamishinan Lafiya
Wadanda suka cancanci gwajin Coronavirus
A yanzu dai jihar Akwa Ibom ta shiga jerin jihohin da aka samu wadanda suka kamu, da mutum biyar.
Tara daga cikin sauran sabbin kamun dai a Legas suke, bakwai a Yankin Babban Birnin Tarayya, daya a Kaduna, daya a Bauci.