Coronavirus: Yawan wadanda suka kamu ya karu da 11
Yawan wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar coronavirus a Najeriya ya karu da mutum 11. Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC), wadda ta bayar da snarwar hakan a shafinta na Twitter, ta ce an samu mutanen 11 ne a jihar Legas. “Zuwa karfe 11.00 na daren 14 ga watan Afrilu, an […]
Yawan wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar coronavirus a Najeriya ya karu da mutum 11.
Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC), wadda ta bayar da snarwar hakan a shafinta na Twitter, ta ce an samu mutanen 11 ne a jihar Legas.
“Zuwa karfe 11.00 na daren 14 ga watan Afrilu, an samu mutum 373 da aka tabbatar sun kamu da #COVID-19 a Najeriya—99 daga cikinsu an sallame su, yayin da 11 kuma suka riga mu gidan gaskiya.
Har yanzu dai jihar Legas ce ke kan gaba a yawan wadanda suka kamu da mutum 214, yayin da Yankin Babban Birnin Tarayya ke bi mata da mutum 58.
Tun bayan da aka samu mutum na farko a Kano ne dai adadin jihohin da ke da wadanda aka tabbatar sun kamu ya kai 20 ciki har da Yankin Babban Birnin Tarayya.