Coronavirus: Za a fitar da almajirai 4,443 daga jihar Nasarawa

Gwamnatin jihar Nasarawa ta kammala shirye-shiryen mayar da almajirai 4,443 zuwa jihohinsu na asali. Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa za a kwashe almajiran, wadanda ba ‘yan asalin jihar ba ne, a mika su ga danginsu. Majiyar ta kara da cewa gwamnatin ta gama shirya motocin da za su yi jigilar almajiran a ‘yan […]

Coronavirus: Za a fitar da almajirai 4,443 daga jihar Nasarawa

Gwamnan Jihar Nasarawa Injiniya Abdullahi Sule

Gwamnatin jihar Nasarawa ta kammala shirye-shiryen mayar da almajirai 4,443 zuwa jihohinsu na asali.

Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa za a kwashe almajiran, wadanda ba ‘yan asalin jihar ba ne, a mika su ga danginsu.

Majiyar ta kara da cewa gwamnatin ta gama shirya motocin da za su yi jigilar almajiran a ‘yan kwanaki masu zuwa.

Gwamnatin za ta mayar da almajiran zuwa jihohi 19 da Yankin Babban Birnin Tarayya Abuja.

Almajirai 207 za a mayar  jihar Adamawa, 701 Bauchi,  34  Binuwai, 24 Borno, 55  Gombe , 273  Jigawa, da kuma guda daya da za a kai jihar Enugu.

Sauran sun hada da 417 da za a kai  Kaduna,  1,497 Kano,  689 Katsina,  208 Kebbi, 35 Kogi, 13 Kwara , 76 Niger, 3 Oyo, 160 Filato, 48 Sakkwato,  102 Taraba, 49 Yobe, 219 Zamfara  da kuma daya da za a mayar Yankin Babban Birnin Tarayya.

A gefe guda kuma, almajirai 24,005 za a mayar  wurin iyayensu a fadin jihar ta Nasarawa.

Sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Ahmad Tijjani Aliyu, ya ce a wani taro da suka gudanar ta yanar gizo, gwamnonin jihohin arewacin Najeriya sun amince da mayar da almajirai zuwa jihohinsu na asali saboda su samu kulawar iyayensu.

Ma’aikatan Abuja ba sa sona — Wike

Boko Haram sun kai hari sansanin sojoji da ofishin ’yan sanda

Mutane Biyu Sun Mutu, Da Dama Sun Jikkata Sakamakon Ruwan Sama A Gashuwa

Gwamnati ta ƙara albashin sojoji — Ministan Tsaro