An bude sabuwar cibiyar killace masu Coronavirus a Legas
Gwamnan Legas Babajide Sanwo-Olu ya kaddamar da cibiyar killace masu cutar Covid-19 mai gadaje 80 da ke Oniru a jihar. Gwamnan ne ya shaida hakan a kafafen sada zumuntarsa. Gwamna Sanwo-Olu ya bayyana cewa za su ci gaba da fadada cibiyoyin killace masu cutar a daidai lokacin da suke cin galaba a yaki da yaduwar […]
Gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu lokacin da ya ziyarci wani wajen killace masu coronavirus
Gwamnan Legas Babajide Sanwo-Olu ya kaddamar da cibiyar killace masu cutar Covid-19 mai gadaje 80 da ke Oniru a jihar.
Gwamnan ne ya shaida hakan a kafafen sada zumuntarsa.
Gwamna Sanwo-Olu ya bayyana cewa za su ci gaba da fadada cibiyoyin killace masu cutar a daidai lokacin da suke cin galaba a yaki da yaduwar annobar.
Ya ce, sun fadada cibiyoyin gwajin cutar zuwa kusa da jama’a kamar yadda yake a cikin tsarin Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC).
- Yawan masu Coronavirus a duniya ya haura miliyan 1
- Coronavirus: Sabbin ka’idojin binne gawa a Legas
- Coronavirus: Yadda aka samu karin majinyata 117
Zuwa yanzu jihar Legas ce a kan gaba a yawan mutanen da suka kamu da coronavirus a Najeriya inda take da yawan wadanda suka kamu mutum 430 cikin mutum 782 da suka kamu a Najeriya.

