COVID-19 a Daura: Yadda aka yi musayar zafafan kalamai

Wata zazzafar muhawara ta barke a jihar Katsina, inda gwamnati ta bayar da umarnin rufe garin Daura bayan da sakamko ya nuna wasu daga cikin iyalan likitan nan da ya rasu sun kamu da coronavirus. Bayan umarnin da Gwamna Aminu Bello Masari ya bayar sanadiyar samun mutum uku a cikin iyalan Dokta Aliyu Yakubu da […]

COVID-19 a Daura: Yadda aka yi musayar zafafan kalamai

Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari

Wata zazzafar muhawara ta barke a jihar Katsina, inda gwamnati ta bayar da umarnin rufe garin Daura bayan da sakamko ya nuna wasu daga cikin iyalan likitan nan da ya rasu sun kamu da coronavirus.

Bayan umarnin da Gwamna Aminu Bello Masari ya bayar sanadiyar samun mutum uku a cikin iyalan Dokta Aliyu Yakubu da kwayar cutar ne, kwatsam sai ga wani bidiyo yana yawo a kafafen sadarwa na zamani.

A cikin bidiyon dai ‘ya’yan marigayin Nura da Abdulmalik Aliyu sun musanta cewa suna dauke da wannan cuta sannan suka nuna shakku a kan sakamakon da aka kawo tun farko na mahaifinsu suna zargin an yi cuwa-cuwa.

Sannan suka ce hukumar NCDC ba ta kira su ba ta ce suna dauke da wannan cuta.

A kan haka suke bayar da sanarwa cewa ko da an ji su shiru to jama’a su san halin da suke ciki, domin a cewarsu ta hannun abokai da masu kiransu a waya suka samu labarin, har ma an ce za a kai su Katsina domin killacewa.

Cece-kuce

Fitar wannan bidiyo ya jawo cece-kuce a tsakanin jama’a, musamman a garin na Daura.

Aminiya ta yi kokarin jin ta bakin wasu daga cikin jama’ar na Daura domin su ne abin ya fi shafa.

Ma’awiyya Mamman Daura na cikin wadanda suke shakkun wancan sakamakon bincike da aka bayar.

A cewarsa, ta yaya za a ce daga cikin mutane 23 da suka yi mu’amulla da marigayin mutum uku kacal ne suke dauke da cutar kuma iyalansa?

“Ina wadanda suka yi mashi wankan gawa, ina sauran mutanen da ya yi harka da su ciki kuwa har da manyan mutane? Duk babu wanda ya kamu sai mutum uku?

“Lallai lamarin akwai alamar tambaya”, inji shi.

Ya kuma ce su a iya sanin su da marigayin da ma can ba shi da lafiya.

“Hasali ma, kowa ya san yana da ciwon hawan jini da kuma na hanta. Sannan kuma kamar yadda muke da labari, har aka rufe shi a kabari bakin shi na zubo da jinni”.

Saboda haka suna ganin wannan lamarin wata balulluba ce dai kawai a hukumance ake so a yi masu, a cewarsa.

Kazalika, wani wanda ya nemi a sakaya sunan shi cewa ya yi kawai gwamnatin jihar Katsina ce ta shirya wannan domin a ba ta kudin tallafin da ake bayarwa saboda yakar wannan cuta.

Ya kara da cewa su har yanzu babu wata alama da suka gani ga wani ko wasu, domin hatta tafiyar da ake cewa Dokta Yakubu ya yi zuwa Legas, sai bayan ‘yan kwanaki da dawowarsa sannan ma waccan rashin lafiyar ta shi ta tsananta.

Sannan kuma in har batun gaskiya ne, me ya sa aka bayar da gawar shi aka rufe tun da ana da wancan zargin?

“Nan muka ji Lai Mohammed yana ta babatu cewa duk wanda cutar coronavirus ta kashe, gwamnati ce ke da hakkin rufe gawarsa domin akwai yadda ake yi. Amma sai ga wannan har sai bayan kwana uku da mutuwarsa sannan a ce cutar ta kashe shi”.

Sabanin ra’ayi

Shi kuwa Malam Hamisu Lawal cewa ya yi, “yana da kyau jama’a su yi taka tsantsan a kan wannan cuta da yadda take yaduwa.

“Ba karyatawa ya kamata a ce muna yi ba, a’a, sai mu fi bayar da hankali a kan daukar matakan kariya da kuma kiyaye duk wata doka da aka shimfida domin hana yaduwar wannan cuta wadda take tabbas akwai ta.

“Ni ina ganin ba uzuri ba ne a ce lallai sai duk wanda ya yi mu’amulla da Dokta Yakubu ya dauki wannan cuta, sannan kuma ba abin mamaki ba ne a ce an samu iyalin shi da cutar, domin sune suka fi kowa kusanci da shi.

“Sannan kuma ba gama binciken aka yi ba balle a ce shi ke nan. Sannan kuma mun ji irin hudubar da Mai Martaba Sarkin Daura Dokta Farouk Umar Farouk ya yi mana a masallaci a kan wannan batu.

“Shin muna tunanin sarki zai bari a cuci talakawan shi?” inji Malam Hamisu.

Martanin gwamnati

Ita kuwa a nata bangaren, dangane da bidiyon yaran, gwamnatin jihar Katsina ta mayar da martani ta bakin Alhaji Abdulhadi Bawa, mai bai wa Gwamna Masari shawara a kan harkokin sadarwa na zamani.

A cewarsa, tun kafin rasuwar Dokta Yakubu, likitocin da ke asibitin da aka kai shi ne suka fara lura da alamomin coronavirus a jikin shi wanda hakan ya sa suka debi jinin shi suka mika wa NCDC domin a gudanar da bincike.

“Hakan ne ya sa gwamnati ta yi gaugawar sawa a nemo duk wani wanda ya yi mu’amala da shi kafin ya mutu, hakan ne ya sa aka samo mutane 23 don a yi masu gwajin da ya samar da sakamakon samun mutune uku na dauke da kwayoyin cutar—yaransa biyu da matarshi.

“Sannan kuma an dauki duk matakan da aka dauka domin a kiyaye lafiyar al’umma tare da su wadanda abin ya shafa.

Kakakin gwamnan ya kuma bayyana mamakinsa da yadda was uke nuna shakku a wannan lamari.

“Amma abin mamaki, sai ga su yaran suna karyata gaskiyar wadannan gwaje-gwaje ba tare da la’akari da abin da ka iya zuwa ko ya dawo ba, duk da yarda da suka yi cewar an dauki jinin mahaifin nasu don gwaji, amma wai anyi cuwa-cuwa a sakamakon.

“Amma abin da ya manta wanda kuma ya kamata jama’a su sani shi ne, shi wancan bincike kwararru ne suka yi tare da kayan aikin da ya fitar da wancan sakamako, sabanin bayanan yaran. Sannan kuma wani abin da jama’a ya kamata su fara yin tunani a kai shi ne, da wane dalili hukumomi za su canza sakamakon mahaifinsu da su kansu ‘yan gidan?

“Akwai wasu dake son saka rudani a cikin al’umma cewa wai gwamnatin jiha ce ke son a kawo mata kudin yaki da wannan cuta daga gwamnatin tarayya shi ya sa ta shirya wannan, amma sai suka gaza tuna cewa, in haka ne, ta yaya za a yi watsi da kudin mutum 20 a dauki na uku kawai, wato a lika cutar ga 20 a ce uku lafiyar su lau?”.

Sauyin ra’ayi

Daga nan sai Alhaji Abdulhadi Bawa ya ce yada irin wadannan labaran ba karamin hadari ba ne domin yana iya sa har wasu su yi shakku a kan cewa ita kanta cutar ba gaskiya ba ce, sai in tayi illa a dawo ana da na sani.

“Sannan hakan na iya sawa a rika kyamar baki musamman in aka lura da irin yadda yaran ke kokarin wawantar da batun ga jama’a”.

Sai dai kuma a lokacin da wakilin Aminiya ke kammala wannan rahoto, sai ya sake yin karo da wani bidiyo na biyu da shi Nura Aliyu ya sake fitarwa a kafofin na sada zumunta, inda yake cewa wancan bidiyo na farko ya yi shi ne ga abokansa wadanda ya nemi da su ajiye shi har sai an ji wani abu ya faru gare su, amma sai suka yi gaugawar sakin shi.

“Amma a yanzu mun fahimci duk yadda abubuwan suke, kuma muna nan a Asibitin Kwararru dake nan Katsina inda aka kebe mu tare da mahaifiyar mu, kuma komi na tafiya daidai, ba mu da wata matsala.

“Jama’a su yi watsi da wancan bidiyon na farko, domin yanzu mun gano gaskiya”, inji Nura Aliyu wanda ya yi magana a cikin harshen Ingilishi.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno