COVID-19: A karon farko an samu majinyata kusan 200 a Legas
Alkaluman Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) na daren Juma’a sun nuna cewa an samu karin wadanda suka kamu a jihar Legas da mutum 179, karo na farko da yawan sabbin majinyatan ya kai haka a lokaci guda a Legas. Kididdigar NCDC din ta tsakar daren 15 ga watan Mayu dai ta […]
Alkaluman Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) na daren Juma’a sun nuna cewa an samu karin wadanda suka kamu a jihar Legas da mutum 179, karo na farko da yawan sabbin majinyatan ya kai haka a lokaci guda a Legas.
Kididdigar NCDC din ta tsakar daren 15 ga watan Mayu dai ta nuna cewa karin mutum 288 ne suka kamu a fadin Najeriya, lamarin da ya kai jimillar wadanda aka tabbatar zuwa 5,445 .
Hukumar ta NCDC ta kuma ce a cikin wannan adadi an rasa mutum 171, yayin da aka sallami majinyata 1,320
Hakan dai na nufin a yanzu haka akwai mutum 3,954 da ke jinya.
Daga cikin sabbin majinyatan dai 179 a jihar Legas suke, 20 a Kaduna, 15 a Katsina da Jigawa, 13 a Borno, da kuma 11 a jihar Ogun.
Sai kuma mutum takwas a jihar Kano, bakwai a Yankin Babban Birnin Tarayya, hudu a Ekiti da Neja, sai Oyo da Delta da Bauchi da ke da mutum uku uku.
Jihar Kwara na da mutum biyu sai Edo da ke da karin majinyaci daya.
Jihar Legas ce dai ke kan gaba a yawan wadanda suka kamu da cutar COVID-19, da adadin majinyata 2,278, sai jihar Kano da ke biye mata da majinyata 761.