COVID-19: Abubuwa biyar da ba a sassauta ba
Har yanzu da sauran rina a kaba bayan sassauta wasu haramcin da gwamnati ta sanya domin hana yaduwar cutar coronavirus. Shugaban kwamtin yakar cutar COVID-19 da shugaban kasa ya nada (PTF) Boss Mustapha ya sanar da sassaucin a jawabinsa. Boss Mustapha ya sanar da bude bankuna da wuraren ibada da kuma rage dokar kulle da […]
Har yanzu da sauran rina a kaba bayan sassauta wasu haramcin da gwamnati ta sanya domin hana yaduwar cutar coronavirus.
Shugaban kwamtin yakar cutar COVID-19 da shugaban kasa ya nada (PTF) Boss Mustapha ya sanar da sassaucin a jawabinsa.
Boss Mustapha ya sanar da bude bankuna da wuraren ibada da kuma rage dokar kulle da sa’o’i hudu.
Ya kamata ku san wadannan abubuwa biyar da gwamnati ba ta janye haramcinsu ba tukuna:
- An janye dokar kulle a Kano
- An bude bankuna, an sassauta dokar kullen COVID-19
- Abin da kungiyoyin addinai suka ce kan bude wuraren ibada
1 — Sufuri tsakanin jihohi
Har yanzu gwamnati ba ta sassauta dokar hana yin tafiya daga wata jiha zuwa wata ba.
“An haramta tafiye-tafiye tsakanin jihohi, sai dai ga masu dakon gayan abinci da albarkatun mai da sauran muhimman kaya,” inji Boss Mustapha.
2 — Tarukan jama’a
Duk da cewa an bude wuraren ibada da tarukan ibada, “taruwar mutum fiye da 20 zai ci gaba da zama haramtacce”, sai dai idan a wurin aiki ne.
3 — Cire takunkumi
Wajibi ne a ci gaba da sanya takunkumi a cikin taron jama’a na tsawon makonni hudu masu zuwa.
Kazalika za a rika auna zafin jiki a wuraren taruwar jama’a.
4 — Sufurin jiragen sama
Tashoshin jirage na cikin gida za su ci gaba da zama a rufe, a cewar Boss Mustapha.
An ba bangaren sufurin jiragen sama umurnin fitar da matakan kariyar da za su ba da damar bude tashoshin jiragen zuwa ranar 21 ga watan Yuni da muke ciki.
5 — Bude makarantu
Ba za a bude makarantu yazu ba da adadin masu cutar coronavirus ya haura 10,000 a Najeriya.
Boss Mustapha ya ce kwamitinsa na aiki tare da Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya domin sake bude makarantun ba tare da wani hadari ba.