COVID-19: Alkawura 6 da Buhari ya yi wa ’yan Najeriya

A jawabin da ya yi wa ‘yan Najeriya da maraicen Litinin, wanda a ciki ya bayyana tsawaita dokar hana fita sam-sam a jihohin Legas da Ogun da kuma Yankin Babban Birnin Tarayya, Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa ‘yan Najeriya, musamman wadanda abin ya shafa, wasu alkawura. Ga biyar daga cikin alkawuran da Shugaba Buhari […]

COVID-19: Alkawura 6 da Buhari ya yi wa ’yan Najeriya

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce gwamnati za ta yi dukkan mai yiwuwa don tallafa wa ‘yan Najeriya

A jawabin da ya yi wa ‘yan Najeriya da maraicen Litinin, wanda a ciki ya bayyana tsawaita dokar hana fita sam-sam a jihohin Legas da Ogun da kuma Yankin Babban Birnin Tarayya, Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa ‘yan Najeriya, musamman wadanda abin ya shafa, wasu alkawura.

Ga biyar daga cikin alkawuran da Shugaba Buhari ya yi:

1- Inganta cibiyoyin kula da wadanda suka kamu da cutar coronavirus

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi alkawarin fadada da samar da kayan aiki ga cibiyoyin kula da wadanda suka kamu, da ma gina wasu a kusa da filayen jiragen sama da iyakokin Najeriya.

“Za mu yi amfani da kudinmu da kuma gudunmawar da muka samu wajen inganta cibiyoyin kula da wadanda suka kamu da cutar cikin makwanni masu zuwa”, inji shi.

2- Ci gaba da raba kayan agaji da kudi

Da yake magana a kan mutanen da sai sun fita za su samu abin da za su ci, Shugaba Buhari ya yi alkawarin ci gaba da bayar da tallafi don rage musu radadi.

A cewar shi, “A makwanni biyun da suka shude mun sanar da raba kayayyakin agaji da suka hadar da kayan abinci da kudi domin saukaka wa jama’a a wannan lokaci mawuyaci. Za a ci gaba da bayarwa”.

3- Fadada rejistar iyalan da ke cikin talauci

Shugaba Buhari ya kuma ce ya sa a fadada rajistar mutanen da suka fi kowa rangwamen gata ta fuskar abin hannu a kasar.

“Na bayar da umarnin kara yawan gidajen marasa galihu daga mutum miliyan 2.6 a yanzu zuwa miliyan 3.6. Wannan na nufin za mu tallafa wa karin gidaje miliyan daya a karkashin tsarin tallafa wa marasa galihu. Wani kwamitin kwararru na aiki a kan haka kuma za su kawo min rahoton su a karshen makwan nan”, inji shugaban kasar.

4- Tallafa wa gwamnonin jihohi

Da yake yaba wa gwamnonin jihohi, musamman saboda yadda suka daidatu sahun manufofinsu da na gwamnatin tarayya, Shugaba Buhari cewa ya yi, “Ina ba ku tabbacin cewa a makwanni masu zuwa gwamnatin tarayya ta hannun Kwamitin Cika-Aiki na Shugaban Kasa, za ta tallafa maku domin idan muka hada hannu za mu gudu tare mu tsira tare a yaki da wannan annoba”.

5- Samar da manufar bunkasa tattalin arzikin kasa

A cewar Shugaba Buhari, babu wata kasa da tattalin arzikinta zai jure matakin hana komai motsawa. Don haka ya yi alkawarin samar da wata manufa da za ta ceto tattalin arzikin Najeriya.

“Zan umarci ministocin ciniki da masana’antu da na sadarwa da na kimiyya da fasaha, da ministan sufuri, da na harkokin cikin gida da na lafiya da na ayyuka da gidaje da na kwadago da ingantuwar aiki da na ilimi su hada hannu su samar da wata manufa wadda za ta shata yadda tattalin arzikin Najeriya zai ci gaba da bunkasa a wannan lokaci na a annoba”.

6- Tabbatar da annobar ba ta shafi noman bana ba

Shugaba Muhammadu Buhari ya kuma yi alkawarin daukar matakan da suka dace don ganin annobar ba ta hana noma ba a bana.

” Zan umarci ministan noma da raya karkara, da mai bai wa shugaban kasa shawara a kan harkar tsaron kasa, da shugaban hukumar kula da albarkatun abinci na kasa da hukuma mai kula da takin zamani a fadar shugaban kasa su yi aiki tare da Kwamitin Cika-Aiki a Kan Yaki da COVID-19 domin ganin annobar ba ta yi tasiri sosai ba a kan harkar noma bana”,

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno