COVID-19: An fasa bude wuraren ibada a Legas

Gwamnatin Legas ta fasa bude wuraren ibada da a baya ta ce za ta yi a yunkurinta na saussauta dokar kullen kare yaduwar COVID-19  a jihar. Gwamnan jihar Babajide Sanwo-Olu ne ya bayyana haka a ranar Talata, 16 ga watan Yuni a jawabin da ya gabatar wa manema labarai kai tsaye ta bidiyo. A baya […]

COVID-19: An fasa bude wuraren ibada a Legas

Gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu

Gwamnatin Legas ta fasa bude wuraren ibada da a baya ta ce za ta yi a yunkurinta na saussauta dokar kullen kare yaduwar COVID-19  a jihar.

Gwamnan jihar Babajide Sanwo-Olu ne ya bayyana haka a ranar Talata, 16 ga watan Yuni a jawabin da ya gabatar wa manema labarai kai tsaye ta bidiyo.

A baya dai gwamnan na Legas ya ce za a bude masallatai a ranar 19 ga watan Yuni, yayin da za a bude coci-coci ranar 21 ga watan, sai dai a yanzu sanarwar baya-bayan nan ta soke hakan.

Jihar Legas ita ce jihar da cutar COVID-19 ta fe kamari a fadin Najeriya kuma a nan aka fara samun bullar cutar.

A ranar Litinin cutar ta yi sanadiyyar mutuwar Dan Majalisar Dattawa mai wakiltar Legas ta Gabas Sanata Sikiru Osinowo.