COVID-19: An killace mutum 99 a Borno

Bayan samun mutum daya da aka tabbatar ya kamu da cutar coronavirus a Maiduguri, hukumomi sun killace mutum 99 don hana yaduwar cutar. Mutanen da aka killace din dai wadanda aka yi amanna sun yi mu’amala da mutumin ne wanda ya rasu yana da shekara 56 ranar Lahadi, bayan an kai shi Asibitin Koyarwa na […]

COVID-19: An killace mutum 99 a Borno

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum

Bayan samun mutum daya da aka tabbatar ya kamu da cutar coronavirus a Maiduguri, hukumomi sun killace mutum 99 don hana yaduwar cutar.

Mutanen da aka killace din dai wadanda aka yi amanna sun yi mu’amala da mutumin ne wanda ya rasu yana da shekara 56 ranar Lahadi, bayan an kai shi Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri saboda yana fama da matsalar da ta shafi numfashi.

Talatin da biyar daga cikin mutanen a kauyen Pulka na karamar hukumar Gwoza suke, sauran mutum 64 kuma a Maiduguri.

An tabbatar marigayin ya kamu da cutar ne bayan da Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta  bayar da sakamakon gwajin da aka yi masa.

Tuni dai aka umarci kungiyar da ya yi wa aiki a Pulka da ta killace duk wani wanda ya yi hulda da shi, sannan ta mika jerin sunayensu ga Kwamitin Yaki da Cutar Coronavirus a jihar Borno don daukar matakin da ya dace

Tuni wasu yan kwamitin suka isa garin Pulka domin gudanar da bincike da dauko samfur na wasu mutanen.

Marigayin, wanda tsohon ma’aikacin jinya ne, kafin rasuwar tasa yana aiki ne da kungiyar likitoci ta Medicines Sans Frontier (MSF) a garin Pulka.

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya