COVID-19: An killace mutum biyu a asibitin Kafanchan
An killace wasu mutum biyu, da da uba, da ake zargin sun kamu da cutar coronavirus a babban asibitin garin Kafanchan da ke karamar hukumar Jama’a a jihar Kaduna. Wani mamba a kungiyar kai daukin gaggawa game da cutar, Dokta Hosea Miwok, ya tabbatar da hakan ga manema labarai a garin na Kafanchan. “Mutum biyun […]
An killace wasu mutum biyu, da da uba, da ake zargin sun kamu da cutar coronavirus a babban asibitin garin Kafanchan da ke karamar hukumar Jama’a a jihar Kaduna.
Wani mamba a kungiyar kai daukin gaggawa game da cutar, Dokta Hosea Miwok, ya tabbatar da hakan ga manema labarai a garin na Kafanchan.
“Mutum biyun sun kawo kansu ne asibitin bayan mahaifin, wanda ya dawo daga Abuja makonni biyu da suka wuce kuma ya killace kansa, ya fara ganin wasu alamomi da suka hada da tari sannan dansa ma ya kama daga baya”, inji Dokta Miwok.
Ya kuma ce alamu sun dada bayyana a asibitin, dalilin da ya sa aka killace mutanen kuma aka sanar da Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) wadda ake sa ran isowar jami’anta ranar Laraba don diban samfur daga gare su da za a kai wurin gwaji.
Kaduna dai na cikin jihohin da aka samu wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar, ciki kuwa har da gwamnan jihar Malam Nasir El-Rufai.
Zuwa karfe 11 na daren Talata mutum shida ne aka tabbatar sun kamu a jihar.