COVID-19: An kwaso ‘yan Najeriya 322 da suka makale a Amurka

An kwaso ‘yan Najeriya 322 da suka makale a kasar Amurka sakamakon bullar cutar coronavirus da ta hana su iya dawowa gida. Hukumar Kula da ‘Yan Najeriya da ke Kasashen Waje (NIDCOM) ta sanar da haka ranar Asabar ta shafinta na Twitter. COVID-19: ‘Yan Najeriya 317 sun dawo daga Birtaniya ‘Yan Najeriya sun yi fatali […]

COVID-19: An kwaso ‘yan Najeriya 322 da suka makale a Amurka

Filin jirgin sama na Murtala Mohammed-(MMIA), Legas

An kwaso ‘yan Najeriya 322 da suka makale a kasar Amurka sakamakon bullar cutar coronavirus da ta hana su iya dawowa gida.

Hukumar Kula da ‘Yan Najeriya da ke Kasashen Waje (NIDCOM) ta sanar da haka ranar Asabar ta shafinta na Twitter.

NIDCOM ta ce ‘yan Najeriyan sun sauka ne a filin jirgi na Murtala Mohmmed da ke Legas.

Ta kara da cewa daga nan za su wuce zuwa inda za a killace su na tsawon kwana 14 kamar yadda Gwamnatin Tarayya ta tsara domin dakile yaduwar cutar ta coronavirus.

Dawowan rukunin da aka kwaso daga Amurkan na zuwa ne kwana shida bayan Gwamnatin Tarayya ta dawo da wasu ‘yan Najeriya 317 daga kasar Birtaniya da bulllar annobar ta hana su baro kasar.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno