COVID-19: Ba a samu sabbin majinyata ba a Kano
A cikin sa’o’i 24 zuwa karfe 11.55 na daren 16 ga watan Mayu, ba a samu ko mutum guda ba da ya kamu da cutar coronavirus a jihar Kano. Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano ce ta bayyana hakan a wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter. Sai dai, a cewar ma’aikatar, an samu […]
A cikin sa’o’i 24 zuwa karfe 11.55 na daren 16 ga watan Mayu, ba a samu ko mutum guda ba da ya kamu da cutar coronavirus a jihar Kano.
Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano ce ta bayyana hakan a wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter.
Sai dai, a cewar ma’aikatar, an samu “karin mutum biyu da suka riga mu gidan gaskiya yayin da aka sallami mutum uku bayan sun warke”.
- COVID-19: Yawan majinyata zai karu a Kano —Ganduje
- ‘Ba za mu yarda da gwajin maganin coronavirus a Kano ba’
Wannan bayani dai ya dace da abin da Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta wallafa, wanda ya nuna babu jihar ta Kano a jerin jihohin da aka samu sabbin majinyata.
A bayanin da NCDC ta wallafa a nata shafin na Twitter dai, a yanzu haka jimillar wadanda aka tabbatar sun kamu da COVID-19 a fadin Najeriya mutum 5,621 ne bayan da aka samu sabbin majinyata 176.
Fiye da rabin sabbin majinyatan dai, wato 95, a jihar Legas suke, yayin da aka samu 31 a jihar Oyo.
Sauran kuwa an same su ne a Yankin Babban Birnin Tarayya (11), da jihohin Neja da Borno (takwas-takwas), da Jigawa (shida), da Kaduna (hudu).
Sai kuma mutum uku a jihar Anambra, bibbiyu a Edo da Ribas da Nasarawa da Bauchi, yayin da Binuwai da Zamfara ke da mutum guda ko wacce.
Zuwa yanzu dai adadin mutanen da suka rasa rayukansu a kasa baki daya ya kai 176; an kuma sallami mutum 1,472 bayan sun warke.