COVID-19: Babban Mufti na Saudiyya ya ce a yi sallar Idi a gida
Babban malami mai ba da fatawa kuma shugaban Majalisar Manyan Malaman kasar Saudiyya Sheikh Abdul Aziz Al Asheikh ya ya ba da fatawa cewa za a iya yin sallar Idi a gida idan akwai wani yanayi na kunci kamar wanda ake ciki na annobar coronavirus. Ita dai sallar Idi raka’a biyu ce kadai da ake […]
Babban malami mai ba da fatawa kuma shugaban Majalisar Manyan Malaman kasar Saudiyya Sheikh Abdul Aziz Al Asheikh ya ya ba da fatawa cewa za a iya yin sallar Idi a gida idan akwai wani yanayi na kunci kamar wanda ake ciki na annobar coronavirus.
Ita dai sallar Idi raka’a biyu ce kadai da ake yin kabbara fiye da sauran sallolin farilla.
Jaridar Okaz/Saudi Gazette ta ambato malamin yana shaida mata cewa za kuma a iya bayar da zakkar fid da kai ta hanyar wasu kungiyoyi muddin an yarda da gaskiyarsu, amma sai dai a bayar kwana guda kafin ranar Sallah.
- Dokar NCDC: ‘Ba mu ba ’yan majalisa na-goro ba’
- Dokar kulle: Masari ya sassauta bayan ya gana da malaman addini
- Ganduje zai sassauta dokar kulle idan ana bin matakan kariya
Malamin ya bukaci iyaye su faranta wa ’ya’yansu da iyalansu rai ta hanyar kashe musu kudi.
Shi ma wani dan Majalisar Manyan Malaman, Sheikh Abdul Salam Abdullah Al-Sulaiman, ya ce mutum zai iya yin sallar Idi shi kadai ko kuma cikin jam’i.
Sheikh Abdul Salam ya bayyana wa jaridar Okaz/Saudi Gazette cewa mai sallar zai fara da kabbarar harama sannan ya biyo ta da kabbarori shida a raka’ar farko kafin karanta suratul Fatiha a bayyane daga nan an so a karanta Surah Al-Qaf.
A raka’a ta biyu kuma za a yi kabbarori biyar bayan ta farko kafin a karanta Suratul Fatiha sannan Surah Al-Qamar kamar yadda Manzon Allah (S.A.W) ya ba da misali.
Ana iya karanta Surah Al-A’la da Al-Ghashiya a maimakon surorin Al-Qaf da Al-Qamar a kowace raka’a.