COVID-19 ce dalilin mace-macen Kano —Dokta Gwarzo

Tawagar da Kwamitin Cika-Aiki na Shugaban Kasa a Kan Yaki da Coronavirus ya tura Kano don tallafawa a yakin da ake yi da coronavirus ya dora alhakin karuwar mace-macen da aka samu a babban birnin jihar a kan cutar. Jagoran tawagar, Dokta Nasiru Sani Gwarzo, ya bayyana hakan a lokacin da a yake tattaunawa da […]

COVID-19 ce dalilin mace-macen Kano —Dokta Gwarzo

Dokta Nasiru Sani Gwarzo

Tawagar da Kwamitin Cika-Aiki na Shugaban Kasa a Kan Yaki da Coronavirus ya tura Kano don tallafawa a yakin da ake yi da coronavirus ya dora alhakin karuwar mace-macen da aka samu a babban birnin jihar a kan cutar.

Jagoran tawagar, Dokta Nasiru Sani Gwarzo, ya bayyana hakan a lokacin da a yake tattaunawa da manema labarai ranar Lahadi yayin mika wani dakin binciken tafi-da-gidanka da Gidauniyar Aliko Dangote ta bai wa gwamnatin Kano.

Ya ce bayan binciken da aka gudanar an gano cewa coronavirus ce ta haddasa da dama daga cikin mace-macen.

“Sakamakon binciken farko-farko ya nuna cewa coronavirus ce ta haddasa [mace-macen].

“Don haka kafin fitowar sakamakon karshe nan da mako guda ko kwanaki kadan masu zuwa, wajibi ne mutanen jihar su farka daga barcin da suke yi su san cewa wannan lamarin ya wuce wasa”, inji Dokta Gwarzo.

A baya dai gwamnatin jihar ta karyata karuwar mace-macen, amma mazauna birnin na Kano sun ci gaba da rayuwa cikin fargaba da rudani, lamarin da ya sa Shugaba Muhammadu Buhari ayyana dokar hana fita a jawabin da ya yi wa ’yan Najeriya a makon jiya, sannan aka tura tawagar don ta gudanar da bincike.

Daya daga cikin ayyukan da aka dora wa tawagar dais hi ne gano musabbabin mace-macen.