‘COVID-19 ce ta yi ajalin Sanata Sikiru Osinowo’
Hukumomi a jihar Legas sun ce cutar COVID-19 ce tayi ajalin Sanata Adebayo Osinowo mai wakiltar Legas ta Gabas a Majalisar Datijjai. Sanata Adebayo Osinowo ya rasu ne a ranar Litinin 15 ga watan Yuni a Asibitin Kwararru da ke Kula da Cututtukan Zuciya, daya daga cikin cibiyoyin killace masu COVID-19 a jihar Legas. Jama’a […]
Hukumomi a jihar Legas sun ce cutar COVID-19 ce tayi ajalin Sanata Adebayo Osinowo mai wakiltar Legas ta Gabas a Majalisar Datijjai.
Sanata Adebayo Osinowo ya rasu ne a ranar Litinin 15 ga watan Yuni a Asibitin Kwararru da ke Kula da Cututtukan Zuciya, daya daga cikin cibiyoyin killace masu COVID-19 a jihar Legas.
Jama’a na ci gaba da tururuwa a gidan mamacin, inda aka killace matarsa a wata mota sannan aka bukaci mutane su yi nesa-nesa da ita, su ba ta tazara.
Shugabar Karamar Hukumar Ikosi-Isheri Uwargida Samiyat Bada, ta yi ta yi wa jama’ar da suka yi cincirindo a gidan gargadi, tana bukatar su koma gida, domin cutar COVID-19 gaskiya ce.
- Sanata Sikiru Osinowo ya riga mu gidan gaskiya
- Majalisa na bincike a kan biliyan 186 na ciyar da dalibai
- Majalisar Dattawa ta yi barazanar ba da umarnin kama Lai Mohammed
“Don Allah ku ja da baya, ina hada ku da Allah, na ga ba kwa ba da tazara, cutar coronavirus gaskiya ce, da ma ku koma gidajenku ku yi masa addu’a a gida da hakan ya fi.
“Za mu sanar da ku shirye-shiryenmu a nan gaba. Muna ba ku shawarar ku yi zamanku ba sai kun zo jana’izarsa ba, domin COVID-19 gaskiya ce, akwai ta”, inji ta.
Hakazalika Bola Ilori Mai Taimaka wa tsohon Gwamnan Jihar Osun kana Ministan Harkokin Cikin Gida Ra’uf Arebgesola ya sanar a shafinta na Facebook cewa COVID-19 ce ta yi ajalin Sanata Osinowo.
“Mun sake rasa wani mutumin kirki a sakamakon coronavirus, wanda jagora ne kuma kusa a jam’iyar APC.
“…Ina maka bankwana Sanata Bayo Osiniwo, ” kamar yadda Bola Ilori ya rubuta a shfinsa na Facebook.
Za a kai gawar marigayin garin Ijebu Ode a jihar Ogun, mahaifarsa ta asali, inda za a yi masa sutura kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.