COVID-19: El-Rufai ya ce zai sake rufe Kaduna idan har…
Gwaman Jihar Kaduna Nasiru El-Eufa’i ya ce zai sake rufe jihar muddin jama’a suka ci gaba da saba ka’idojin kariyar cutar COVID-19. Ya ce idan aka kai matakin da yaduwar cutar ta fi ƙarfin cibiyoyin lafiyar da ma’aikatan lafiya a jihar, dole ya sake sa dokar hana fita. El-Rufa’i ya bayyana haka ne yayin kaddamar […]
Gwaman Jihar Kaduna Nasiru El-Eufa’i ya ce zai sake rufe jihar muddin jama’a suka ci gaba da saba ka’idojin kariyar cutar COVID-19.
Ya ce idan aka kai matakin da yaduwar cutar ta fi ƙarfin cibiyoyin lafiyar da ma’aikatan lafiya a jihar, dole ya sake sa dokar hana fita.
El-Rufa’i ya bayyana haka ne yayin kaddamar da dakin gwajin COVID-19 na tafi da gidanka wadda Hukumar USAID ta ba wa jihar.
“A baya mun saukaka dokar kullen ne saboda mun gamsu da tsarin gwaji da muke yi, sannan kuma da wadatattun kayan gwajin da kyakkyawan tsarin kiwon lafiya.
- El-Rufai ya sauya dokar kullen coronavirus
- El-Rufai ya bude masallatan Juma’a
- Dokar kulle: Ba a bude masallacin Sultan Bello a Kaduna ba
“Don haka ina kira ga al’ummar Jihar Kaduna da su ci gaba da bin matakan kariya, su kuma guji yawan fita har sai yin haka ya zama dole.
“Idan bukatar sake kulle jihar ta taso, ba za mu yi kasa a gwiwa ba, za mu sake rufe ta. Gara mu tsare lafiyar al’ummarmu, in ya so daga baya sai mu nemi afuwarsu”, inji shi.
Nasir El-Rufa’i ya ce dakin gwajin tafi-da-gidankan a cikin babbar mota, Gwamanatin Amurka ce ta ba wa jihar ta hannun hukumar USAID domin yin gwajin cutar tarin fuka.
Amma bullar coronavirus ta sa aka yi shawarar yin amfani da ita wajen gwajin cutar, wadda ya ce har an yi wa sama da mutum 200, wadanda mafi akasarinsu aka samu suna dauke da ita.
Zuwa lokacin haɗa wannan rahoto mutum 513 ne aka tabbatar sun kamu da cutar coronavirus a jihar Kaduna. Mutum 286 sun warke sai mutum 10 da ta yi ajalinsu a jihar.