COVID-19: Gwamnan Ribas ya yi barazanar dawo da dokar kulle
Gwamnan ya ce tilas ne a bi doka ko kuma dokar kulle ta fara aiki.
Gwamnan Ribas, Nyesom Wike, ya yi barazanar dawo da dokar kulle a jihar matukar jama’a suka ci gaba da yin burus da matakan kariyar cutar COVID-19.
Wike ya bayyana hakan ne a jawabina ga jama’ar jihar a ranar Litinin, inda ya ce alkaluman da hukumar NCDC mai kula da yaduwar cututtuke take fitarwa kullum na nuna cewa ana samun karuwar masu harbuwa da kuma mutuwa a sanadiyyar cutar.
Gwamnan ya ce duk da cewa gwamnatinsa za ta so ta kyale jama’a su ci gaba da al’amuransu na ibad, kasuwanci da sauransu, amma hakan ba zai hana ta sake dawo da dokar kulle ba matukar aka ci gaba da yin watsi da matakan kariyar cutar.
“Za mu iya dawo da dokar kullen COVID-19 matukar alkaluma suka ci gaba da nuna ana kara samun masu dauke da cutar, in har hakan ya wuce kima.
“Ba za mu zura ido muna gani ana ci gaba da jefa rayuwar al’umma cikin hadari ba.
“Ina so na tunatar da mutane muhimmancin bin matakan kariyar COVID-19 da suka hada da wanke hannu, sanya takunkumi, guje wa cunkoso, da kuma zuwa yin gwaji da zarar an ji wani sauyi na daban,” inji gwamnan.
Sannan ya roki jama’ar jihar da su zama masu kokarin kare kansu da ’yan uwansu ta hanyar yin allurar rigakafin COVID-19 musamman a cibiyoyin da aka tanadar a kananan hukumomi 23 da ke fadin jihar.