COVID-19: Gwamnonin Najeriya sun kuduri aniyar rufe jihohi
Gwamnonin Najeriya 36 sun amince su aiwatar da dokar hana zirga-zirga a tsakanin daukacin jihohinsu har tsawon mako biyu da nufin hana yaduwar cutar coronavirus. Gwamnonin sun yanke wannan shawara ne bayan sun saurari jawabai daga takwarorinsu na jihohin Legas, da Bauci, da Oyo, da Ogun a kan darussan da suka koya a yakin su […]
Gwamnonin Najeriya 36 sun amince su aiwatar da dokar hana zirga-zirga a tsakanin daukacin jihohinsu har tsawon mako biyu da nufin hana yaduwar cutar coronavirus.
Gwamnonin sun yanke wannan shawara ne bayan sun saurari jawabai daga takwarorinsu na jihohin Legas, da Bauci, da Oyo, da Ogun a kan darussan da suka koya a yakin su da cutar yayin taronsu na shida ta hanyar sadarwar bidiyo (teleconference a Ingilishi).
Wata sanarwar bayan taro da Kungiyar Gwamnonin Najeriya ta fitar ta hannun shugabanta Gwamna Kayode Fayemi na jihar Ekiti ta ce wadanda ayyukansu suka zama lallai da tilas ne kadai za a kyale su fita.
Gwamnonin sun kuma yi kira da a bullo da wani tsari na bai-daya na yakar cutar ta COVID-19 a matsayin hanya mafi inganci ta hana ta yaduwa.
Kungiyar Gwamnonin ta kuma nuna damuwa da yadda ma’aikatan lafiya ke kamuwa da cutar, ta kuma sha alwashin yin aiki da Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) don tabbatar da cewa an sama musu kayan kariya an kuma ba su horo a kai a kai.
Sannan gwamnonin na Najeriya sun kuduri aniyar kafa kwamitocin yaki da cutar a matakan shiyya a karkashin jagorancin kwamishinoninsu na lafiya da nufin karfafa gwiwar aiwatar da shawarwarin hukumomin lafiya a fadin jihohin.