COVID-19: Jihar Osun na raba shinkafa buhu 40,332 ga mabukata

Ta fitar da tsari don tabbatar da rabon ya kai ga kowane bangare

COVID-19: Jihar Osun na raba shinkafa buhu 40,332 ga mabukata

Gwamnatin Osun ta fara rabon buhunan shinkafa dubu arba’in da 333 ga jama’ar jihar domin saukaka musu radadin annobar COVID-19.

Wadanda za su samu tallafin sun hada da marasa galiyu, nakasassu, tsofaffin ma’aikata, malaman addinin Musulunci da na Kirista, da kuma maza da mata.

Shugaban Kwamitin Sanya Ido a kan rabon tallafin, Mista Ademola Adebisi, a ranar Alhamis, ya ce Gwamnatin Jihar ta yi tsari da yadda kowane bangare a jihar zai ci moriyar tallafin.

Ya kara da nuna farin cikinsa na ganin yadda rabon kayan tallafin ke tafiya bisa tsari.

A cewarsa tsarin da aka bi wajen rabon kayan tallafin zai tabbatar da cewar kowane bangare ko yanki na jihar ya samu na rabonsa.