COVID-19: Kaduna za ta bari a yi kasuwanci

Gwamnatin jihar Kaduna na kokarin samar da wani tsari da zai bai wa ’yan kasuwa da sauran wadanda ayyukansu suka wajaba damar gudanar da harkokinsu a lokutan dokar hana fita. Mataimakiyar gwamnan jihar, Dokta Hadiza Balarabe, wacce ta fadi hakan a wani jawabi da ta yi ga al’ummar jihar, ta ce an yanke shawarar ne […]

COVID-19: Kaduna za ta bari a yi kasuwanci

Dokta Hadiza Balarabe, mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna

Gwamnatin jihar Kaduna na kokarin samar da wani tsari da zai bai wa ’yan kasuwa da sauran wadanda ayyukansu suka wajaba damar gudanar da harkokinsu a lokutan dokar hana fita.

Mataimakiyar gwamnan jihar, Dokta Hadiza Balarabe, wacce ta fadi hakan a wani jawabi da ta yi ga al’ummar jihar, ta ce an yanke shawarar ne don a kauce wa fadawa cikin yanayin karancin abinci da abin sha da magunguna.

Ta kuma ce za a kyale ’yan kasuwa su gudanar da harkokinsu ne “saboda muhimmancinsu ga rayuwa, da lafiya, da kuma jin dadin al’ummarmu, amma suna bukatar izini na musamman kafin a kyale su”.

Mataimakiyar gwamnan, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito, ta kuma ce ana sa ran harkokin kasuwancin da suka shiga wadannan azujuwa su mika takardar neman izini ga Ma’aikatar Kasuwanci, Kirkire-kirkire da Fasaha, wadda za ta ba da lasisi bayan ta gudanar da binciken da ya dace.

Dokta Hadiza ta jaddada cewa gwamnati ba za ta sassauta ba a kan matsayinta game da hana yaduwar COVID-19 ta fuskar tarukan jama’a da nisantar juna ko da an ba da takardun izinin.

Kaduna dai na cikin jihohin da suka ayyana dokar takaita hadahada suka kuma rufe iyakokinsu.