COVID-19: Kano ta samu tallafin Dala miliyan daya
Mutanen da COVID-19 ta fi jefawa cikin matsi da kananan da matsakaitan masana’antu za su amfana
Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje
Tarayyar Turai (EU) da Gwamnatin Kasar Japan sun ba wa Jihar Kano tallafin Dala miliyan 1.1 domin rage radin annobar COVID-19 a Jihar.
Sakataren Yada Labarai na Gwamna Abdullahi Ganduje, Abba Anwar ya ce tallafin da aka kebe domin masu kanana da matsakaitan sana’o’i zai taimaka wajen farfadowar al’ummomin da annobar ta yi wa illa sosai.
- Obadiah Mailafia karya ya yi min – Shaikh Dahiru Bauchi
- Batanci: UNICEF ta bukaci soke hukuncin kotun Musulunci
- Za mu daure masu kasuwanci a titin jirgin kasa —Amaechi
Sanarwar da ya fitar ta ce mutun 1,600 za su ci gajiyar tallafin a matsayin ma’aikata, baya ga kanana da matsakaitan masana’antu 630 a fadin jihar.
Ya ce tuni Gwamna Ganduje ya bayar da umarnin mayar da akalar tallafin ga mutanen da suka fi shiga cikin matsi sakamakon bullar cutar ta COVID-19.