COVID-19: Likitocin China za su zo Najeriya
Likitocin China 18 na kan hanyar zuwa Najeriya don taimakawa a yakin da kasar ke yi da annobar coronavirus ko COVID-19. Likitocin za su kuma taho da tsarabar magunguna da kayan aiki, ciki har da na’urorin numfashi wato ventilators da kayan kare kai daga daukar kwayoyin cutar. Ministan Lafiya na Najeriya, Dokta Osagie Ehanire, wanda […]
Likitocin China 18 na kan hanyar zuwa Najeriya don taimakawa a yakin da kasar ke yi da annobar coronavirus ko COVID-19.
Likitocin za su kuma taho da tsarabar magunguna da kayan aiki, ciki har da na’urorin numfashi wato ventilators da kayan kare kai daga daukar kwayoyin cutar.
Ministan Lafiya na Najeriya, Dokta Osagie Ehanire, wanda ya bayyana hakan yayin bayanin da Kwamitin Cika-Aiki na Shugaban Kasa Kan Yakar COVID-19 ya saba yi a Abuja, ya kuma ce wasu ’yan China da ke Najeriya ne suka dauki nauyin wannan tallafi.
“An sanar da ni cewa wata kungiyar kamfanonin China da ke aiki a nan Najeriya za ta taimaka da magunguna da kayan aiki. Wani jirgin sama na musamman mai daukar kaya zai tashi daga Najeriya nan da ‘yan kwanaki don kwaso kayan.
“Sannan wani ayarin kwararru 18 da suka hada da likitoci, da nas-nas, da sauran masana za su biyo jirgin don su taimaka mana”, inji ministan.
Ministan ya kuma yaba wa ma’aikatan lafiya na Najeriya bisa kokarin da suke yi na ganowa da kula da wadanda suka kamu.
Ya kuma ce za a samu karuwar wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar duk da hana fita ko hadahada saboda ana kara gano mutanen da suka yi mu’amala da wadanda suka kamu, ana kuma kara yawan mutanen da ake yi wa gwaji.
Wasu ’yan Najeriya dai na ta kiraye-kiraye ga hukumomi da su kara yawan cibiyoyin yin gwajin su kuma bude kofofin su ga kowa a matsayin hanya mafi inganci ta shawo kan cutar saboda ba a iya sanin masu dauke da ita har sai wasu alamu sun bayyana lokacin su ma sun harbi wasu.