COVID-19: Majinyata kusan 100 sun warke cikin kwana biyu a Legas

Ma’aikatar lafiya ta jihar Legas ta ba da sanarwar karin majinyata 37 da suka warke daga coronavirus. Sanarwar da ma’aikatar ta wallafa a shafinta na Twitter da yammacin Laraba  ta ce 19 daga cikin majinyatan da suka warke mata ne, sai maza 18 da kuma dan kasar Indiya mutum guda. Biyar daga cikin majinyatan an […]

COVID-19: Majinyata kusan 100 sun warke cikin kwana biyu a Legas

Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu a lokacin da ya kaddamar da sabuwar cibiyar killace masu dauke da coronavirus ta Gbagada

Ma’aikatar lafiya ta jihar Legas ta ba da sanarwar karin majinyata 37 da suka warke daga coronavirus.

Sanarwar da ma’aikatar ta wallafa a shafinta na Twitter da yammacin Laraba  ta ce 19 daga cikin majinyatan da suka warke mata ne, sai maza 18 da kuma dan kasar Indiya mutum guda.

Biyar daga cikin majinyatan an sallame su ne daga asibitin kula da masu dauke da  cututtuka masu yaduwa ta Yaba, sai 25 daga cibiyar killace masu cutar ta Onikan, da  kuma bakwai daga cibiyar da ke Eti-Osa.

Majinyata 97 suka warke aka kuma sallame su cikin kasa da kwanaki biyu a Legas, domin asanarwar da gwamnan jihar Babajide Sanwo-Olu, ya fitar a ranar Talata, 5 ga watan Mayu.

Ya shaida cewa majinyata 60 sun warke, maza 40, mata 20, wadanda aka sallama suka  koma cikin iyalansu.

Kawo yanzu majinyata 358 suka warke aka kuma sallame su a Legas, jihar da ke kan gaba a yawan wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos