COVID-19: Masu dauke da cutar sun haura 4000 a Najeriya
Wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar coronavirus sun haura mutum 4,000 a Najeriya. Kididdiga ta baya-bayan nan da Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta wallafa sun nuna cewa tsakar daren 9 ga watan Mayu, an tabbatar da karin mutum 239 da suka kamu da cutar, lamarin da ya sanya masu […]
Wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar coronavirus sun haura mutum 4,000 a Najeriya.
Kididdiga ta baya-bayan nan da Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta wallafa sun nuna cewa tsakar daren 9 ga watan Mayu, an tabbatar da karin mutum 239 da suka kamu da cutar, lamarin da ya sanya masu dauke da COVID-19 suka ketara wannan adadi.
Alkaluman na hukumar NCDC dai sun nuna cewa jimilla mutum 4,151 aka tabbatar sun kamu da cutar a Najeriya zuwa yanzu.
Daga cikin wannan adadi kuwa, mutum 128 sun riga mu gidan gaskiya, yayin da aka sallami mutum 745 bayan sun warke.
Mutum 97 daga cikin sabbin kamun, kamar yadda alkaluman suka nuna, a jihar Legas suke, 44 a Bauchi, 29 a Kano, 19 a Katsina, 17 a Borno, bakwai a Yankin Babban Birnin Tarayya.
Sai kuma jihar Kwara mai mutum shida, Oyo mai biyar, Kaduna da Sakkwato na da uku uku.
Biyu a jihohin Ogun, da Adamawa, da Kebbi, sai jihar Ekiti da ke da mutum daya da ya kamu da cutar.