Covid-19: Mutum 138 ne suka warke a Legas

Gwamnatin jihar Legas ta sallami karin mutum 15 da suka warke daga annobar coronavirus. Daya daga cikin su dan kasar Indiya ne, yayin da ragowar 14 ‘yan Najeriya ne wadanda aka sallama a yau ranar  Litinin 27 ga watan Afrilu. An sallame su ne daga inda da aka killace su a cibiyar kula da cututtuka […]

Covid-19: Mutum 138 ne suka warke a Legas

Gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu lokacin da ya ziyarci wani wajen killace masu coronavirus

Gwamnatin jihar Legas ta sallami karin mutum 15 da suka warke daga annobar coronavirus.
Daya daga cikin su dan kasar Indiya ne, yayin da ragowar 14 ‘yan Najeriya ne wadanda aka sallama a yau ranar  Litinin 27 ga watan Afrilu.

An sallame su ne daga inda da aka killace su a cibiyar kula da cututtuka masu yaɗuwa ta IDH da ke Yaba da kuma wasun su daga cibiyar killace masu cutar da ke sitadiyom ta Mobolaji Johnson.

Sanarwar wacce Gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu da ma’aikatar lafiya ta jihar suka fitar a shafinsu na tweeter ta bayyana cewa 11 daga cikin mutanen da suka warke a wannan karon mata ne, 4 kuma maza.

Kawo yanzu dai mutum 138 ne suka warke daga coronavirus a jihar Legas.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos