COVID-19: ‘Bai dace a sassauta dokar takaita hadahada ba’
Masana kiwon lafiya sun yi gargadi game da matakan da wasu jihohi a Najeriya ke dauka na yin sassauci a kan dokar da suka ayyana ta takaita haduwar jama’a da kuma hada-hada don hana yaduwar annobar coronavirus. Tuni dai wasu jihohi da suka hada da Kaduna da Katsina da Neja da Kogi da Ondo da […]
Masana kiwon lafiya sun yi gargadi game da matakan da wasu jihohi a Najeriya ke dauka na yin sassauci a kan dokar da suka ayyana ta takaita haduwar jama’a da kuma hada-hada don hana yaduwar annobar coronavirus.
Tuni dai wasu jihohi da suka hada da Kaduna da Katsina da Neja da Kogi da Ondo da Rivers da Taraba, suka sassauta dokar bayan korafe-korafe daga al’ummominsu na neman damar fita don sayen kayan abinci ko neman kudin sayansa.
Sai dai a zantawarsa da Aminiya kan matakin jihohin, Dokta Nasiru Sani Gwarzo, wanda masani ne a bangaren kiwon lafiyar al’umma, ya ce ya kasa gane hikimar wannan shawara da jihohi ke yankewa, yana gargadi cewa makwanni biyu masu zuwa suna da muhimmanci.
“Duk matsalar da mu ke ji a yanzu ta karuwar cutar nan, ba ta wuce matakin yada ta daga mutum guda zuwa wani mutumin ba.
“To a makwanni biyu da ke tafe ne idan aka samu akasi za a iya shiga matakin yaduwa daga al’umma zuwa wata al’umma, wato matakin unguwa ke nan.
“Wannan mataki yana da muni musamman ma a kasashe irin namu”, inji Dokta Gwarzo.
- Coronavirus: Za a ci gaba da yin Sallar Juma’a a Katsina
- Coronavirus: Jama’a sun samu walwala a Jalingo
Masanin ya kuma ce kamata ya yi abin da ke faruwa a wasu kasashe kamar yadda kowa ke gani, ko ji ya zama izna ga ‘yan Najeriya.
“Lallai abu ne mai wuya a hana jama’a fita gaba daya musamman bangaren zuwa kasuwa don sayen kayan abinci ko neman na abjnci.
“Abin da ya kamata a karfafa shi ne bin ka’idojin kiwon lafiya na ba da tazarar al’umma tsawon mita biyu”, a cewar kwararren likitan kuma masani a kan lafiyar al’umma.
Ya kuma yi bayani a kan yadda za a gane tazarar mita biyu a saukake.
“Yadda za ka gane mita biyu ba tare da amfani da ma’auni ba kuwa shi ne, babban mutum ya ware hannuwansa biyu, to idan ka auna daga kan yatsun hannun dama zuwa na hagu, shi ne zai baka hakan. Haka nan ka iya gane hakan da taku shida”, inji Dokta Gwarzo.
Dokta Nasiru Sani Gwarzo ya kuma shawarci jama’a da su aiwatar da hakan a cikin gidajensu kamar a dakin kwana ko falo, sannan a rika bude taga da kuma kunna fanka idan akwai wuta.
“Yin hakan ko da a cikin mota ne zai taimaka iska ta busar da kwayar cutar ta mutu ta yadda ko da iska ta dauketa ba ta da sauran tasiri”.
Haka nan ya bukaci jama’a da su rika sa amawali a fuskokinsu yana mai cewa hakan zai yi tasiri wajen hana mai dauke da cutar yada ta, haka nan daga bangaren wanda bai da ita, zai yi tasiri wajen hana saukar ta a kan baki ko hanci.
Ita ma wata gamayyar kungiyoyin farar hula masu fafutukar kawo sauyi a harkar kiwon lafiya, wato Health Sector Reform Coalition ko HSRC a takaice, ta fitar da sanarwa ranar Juma’a tana gargadin gwamnoni da su guji yin sassauci a dokar takaita hada-hadar jama’a.
Wasu jihohin dai kamar yadda suka yi bayani sun dauki matakin ne don bikin ista na mabiya addinin Kirista, yayin da wasu jihohin kuma irinsu Katsina suka kafa hujja da korafe-korafen jama’a kan rashin ba da damar yin sallar juma’a.
Sai dai a cewar kungiyar HSRC, adadin jama’a masu yawa na iya kamuwa da cutar ba tare da nuna wata alama ba, a saboda haka ta bukaci gwamnatocin jihohi da su yi dukkan mai yiwuwa wajen ganin ba a sassauta dokar ba.
A maimakon hakan, ta bukaci gwamnonin da su taimaka wa mabukata a cikin al’ummarsu da kayan abinci.
Galibin jihohin Najeriya dai sun kafa dokar hana ko takaita fita da nufin dakile yaduwar annobar coronavirus.