COVID-19: ‘Plateau na bincike kan kwarmata sakamakon gwaji’
Gwamnatin jihar Filato ta kaddamar da bincike don gano wanda ya saki sakamakon gwajin da aka yi a kan wasu mutane da aka yi zargin sun kamu da cutar coronavirus. Gwamnatin ta kuma tabbatar da cewa duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci fushin hukuma. Kwamishinan Yada Labarai Dan Manjang ne ya fadi haka […]
Gwamnatin jihar Filato ta kaddamar da bincike don gano wanda ya saki sakamakon gwajin da aka yi a kan wasu mutane da aka yi zargin sun kamu da cutar coronavirus.
Gwamnatin ta kuma tabbatar da cewa duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci fushin hukuma.
Kwamishinan Yada Labarai Dan Manjang ne ya fadi haka a wata sanarwa, wadda a ciki ya ce lamarin ba kawai saba ka’idar aiki ya yi ba, zai kuma sanya wadanda abin ya shafa su fuskanci tsangwama da kyama.
“Gwamnati ta yi Allah-wadai da wannan lamari wanda ka iya jefa yunkurin da take yi na yaki da annobar coronavirus cikin garari.
“Don tabbatar da cewa hakan bai sake faruwa ba, tuni gwamnati ta kaddamar da bincike mai zurfi a kan lamarin da nufin bankado wadanda ke da hannu da kuma ladabtar da su yadda ya dace”, inji Mista Manjang.
- Hotuna: Yadda dokar hana fita ta kasance a Plateau
- Coronavirus: Yadda wasu masallatai suka bijire a Jos
Kwamishinan ya yi karin bayani da cewa binciken zai kunshi dukkan matakai kama daga kan daukar kwayoyin halittar wadanda aka yiwa gwajin har zuwa fitar da sakamakon, sannan ya tabbatar wa jama’a cewa an riga an dauki matakin hana faruwar irin haka a gaba don haka kada su karaya.
An dai yi gwajin ne a cibiyar gwajin cutar da ke Cibiyar Binciken Cututtukan Dabbobi ta Kasa (NVRI) a Vom kusa da Jos, babban birnin jihar.
Sakamakon, da ma sunayen mutanen biyu, sun yadu kamar wutar daji a shafukan sadarwa na zamani tun ma kafin a bayyana a hukumance.