COVID-19: Plateau na neman masu alaka da majinyaci na farko

Gwamnatin Filato ta fara bibiyar mutanen da suka yi mu’amala da mutum na farko da aka tabbatar yana dauke da cutar coronavirus a jihar. Kwamishinan lafiya na jihar, Dokta  Ninkong Lar Ndam, wanda ya fadi hakan a wata sanarwa, ya ce gwamnatin za ta kuma dauki wasu Karin matakan kare lafiyar al’umma don tabbatar da […]

COVID-19: Plateau na neman masu alaka da majinyaci na farko

Gwamna Simon Bako Lalong na Jihar Filato

Gwamnatin Filato ta fara bibiyar mutanen da suka yi mu’amala da mutum na farko da aka tabbatar yana dauke da cutar coronavirus a jihar.

Kwamishinan lafiya na jihar, Dokta  Ninkong Lar Ndam, wanda ya fadi hakan a wata sanarwa, ya ce gwamnatin za ta kuma dauki wasu Karin matakan kare lafiyar al’umma don tabbatar da cewa cutar ba ta yadu a yankinta ba.

A daidai lokacin da gwamnatin jihar ta Filato ke sake dage dokar da ta ayyana ta hana fita zuwa ranar Litinin ne dai aka samu mutumin da aka tabbatar ya kamu.

Dokta Ndam ya ce mutumin ya fito ne daga Kano zai shigo garin Jos a ranar 17 ga watan Afrilun nan, amma jami’an kiwon lafiyar jihar suka killace shi.

Kwamishinan ya kara da cewa an killace mutumin ne a cibiyar binciken cutar coronavirus da aka bude a Vom kusa da birnin na Jos, bayan da aka ga ya nuna alamomin wannan cuta.

Kwamishinan ya kuma ce a ranar Alhamis Hukumar Yaki da Cututtuka masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta tabbatar da cewa wannan mutum yana dauke da cutar.

Ya ce tuni an killace mutumin ana yi masa jinya.

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya