COVID-19: Sabbin dokokin bude masallatai da coci-coci

Daga yanzu ya zama wajibi ga wuraren ibada su cika sharudda 29 na bayar da tazara domin kare masu bauta daga kamuwa da annobar COVID-19. Cika sharuddan shi ne zai bayar da damar bude masallatai da coci-coci Babban Birnin Tarayya Abuja. Hukumar Kula da Birnin Tarayya ta ce riga ta tattauna da shugabannin Musulunci da […]

COVID-19: Sabbin dokokin bude masallatai da coci-coci

Babban Masallacin Kasa da Cocin Kasa a Abuja

Daga yanzu ya zama wajibi ga wuraren ibada su cika sharudda 29 na bayar da tazara domin kare masu bauta daga kamuwa da annobar COVID-19.

Cika sharuddan shi ne zai bayar da damar bude masallatai da coci-coci Babban Birnin Tarayya Abuja.

Hukumar Kula da Birnin Tarayya ta ce riga ta tattauna da shugabannin Musulunci da na Kirista kuma sun amince da matakan da aka tsara kafin a bude wuraren ibada.

Ga dokokin nan a jere:

  • Wajibi ne wuraren ibada su samar da ruwa mai gudana da sunadaren wanke hannu a kokofi da sauran wuraen da mutane ke yawan haduwa, ciki har a ban daki.
  • Dole masu ibada su tsaftace hannayensu kafin su shiga.
  • Amfani da takunkumi a rufe fuska jazaman ne.
  • A nisanci cudanya —shan hannu, rungumar juna, ko yin tarayya a kan kayan amfani kamar shinfida, kayan kida, ko makirfon.
  • Wuraren ibada su takaita yawan masu shiga cikinsu ta yadda za a samu tazarar mita biyu a tsakanin masu ibada.
  • Limamai su yi amfani da zanen shimfidu ko na dabe a matsayin alamar tazarar da za a bayar. Sannan su shawarci ‘yan gida daya su zauna kusa da juna.
  • A rage yawan ma’aikatan zuwa adadin da ake bukata kadai, sannan banda masu fama da wata cuta ko dan sama da shekaru 55 a cikinsu.
  • A takaita tsawon lokacin taruwar masu ibada zuwa lokutan yau da kullum kadai.
  • Coci-coci za su bude daga 5:00 na safe zuwa 8:00 na dare. Kada tsayin kowace ibada ya haura awa guda, tare da tazarar minti 30 a tsakani domin kashe kwayoyin cuta.
  • Za a bude masallatai minti 15 kafin lokacin sallah a kuma rufe su bayan minti 10 da sallame sallolin farilla.
  • A taikata lokacin jira tsakanin salloli zuwa minti 10, a kuma gajarta salloli domin rage tsawon lokacin taruwar jama’a.
  • Masallatan juma’a za su bude minti 20 kafin sallah su kuma rufe minti 20 bayan an idar. Kada tsawon lokacin sallar juma’a har da huduba ya haura awa daya.
  • Makarantun Islamiyyah da na coci-coci da ibadar tsakar dare da harkokin kananan yara za su ci gaba da zama a rufe.
  • Sallolin farilla biyar na kowace rana kadai za a rika yi a masallatai.
  • Ba a yarda a gudanar da tarukan jama’a masu wuyar tabbatar da bayar da tazara ba.
  • Za a dan sauya lokutan ibada domin samar da damar bayar da tazara a tsakanin mutane.
  • Masu ibada su halarci lokacin bautar da suka fi zaba, sannan a samar da hanyoyin zamani na yin ibada daga nesa.
  • Wuraren ibada su ware kofofin shiga daban da na fita tare da saukaka shige da fice domin kawar da cinkoso.
  • An haramta dukkan taruka kafin ko bayan gudanar da ibada.
  • Shaguna da cibiyoyin kasuwanci da ke harabar wuraren ibada za su ci gaba da kasancewa a rufe.
  • Mutane masu rauni—’yan shekara 55 zuwa sama, masu matsalar gani, masu raunin garkuwar jiki da masu fama da cutar suga ko ta zuciya—su zauna a gida su yi ibadarsu.
  • Wuraren bauta su cire shimfidunsu domin saukaka kashe kwayoyin cuta.
  • A bar tagogi a bude a lokacin ibada sannan a yi amfani da harabar wuraren bauta.
  • A yawaita tsaftacewa da kashe kwayoyin cuta a wuraren da ake yawan tabawa ko ake yawan amfani da su.
  • Masu tsaftace wuri su rika goge wurare da sunadaren kashe kwayar bayan sun kawar da dauda. Wadanda suka kamu su zauna a waje domin kada su yada cutar.
  • Duk wanda ya ji alamun cutar COVID-19 to nisanci halartar tarukan ibada da kansa.
  • Kada a bari masu bautar da aka lura zafin jikinsu ya wuce kima ko suka nuna alamun COVID-19 su shiga wuraen bauta.
  • A ajiye sunaye da cikakken bayanan ma’aikata da mahalarta kowace ibada da ma adireshinsu domin tuntubar su idan sun yi mu’amala da mai cutar.
  • Limaman addini su nisanci kai ziyara zuwa gidajen mabiya.