Covid-19: Sabbin matakan kariya da Gwamna El-Rufai ya gindaya a Kaduna

Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai, ya rattaba hannu kan wata sabuwar doka wacce ta umarci dukkan wuraren bauta da majami’u da su tilasta wa masu bauta yin amfani da takunkumin rufe fuska, sunadarin tsaftace hannu da kuma bayar da tazara a tsakanin masu bautar a matsayin wani mataki na dakile yaduwar cutar Coronavirus. Sabuwar […]

Covid-19: Sabbin matakan kariya da Gwamna El-Rufai ya gindaya a Kaduna

Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai

Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai, ya rattaba hannu kan wata sabuwar doka wacce ta umarci dukkan wuraren bauta da majami’u da su tilasta wa masu bauta yin amfani da takunkumin rufe fuska, sunadarin tsaftace hannu da kuma bayar da tazara a tsakanin masu bautar a matsayin wani mataki na dakile yaduwar cutar Coronavirus.

Sabuwar dokar ta kuma jaddada cewa a takaita yawan masu ibada a masallatai da sauran majami’u tare da cewa kada a wuce sama da sa’a daya a wuraren bautar.

Wata sanarwa da mashawarcin gwamnan na musamman a kan harkokin yada labarai da sadarwa, Muyiwa Adekeye ya fitar ta ce, sabuwar dokar ta kuma hana manyan taruka da umarnin cewa dole ’yan kasuwa su samar da ma’aunin dumin jiki da sunadarin tsaftace hannu da kuma tabbatar da an kiyaye dokar bayar da tazara da yin nesa-nesa da juna a shagunansu.

A cewarsa, ya zama tilas a rika amfani da takunkumin rufe fuska wanda ya wadatu wajen rufe hanci da baki, kuma kungiyoyi da daidaikun al’umma da suka ba mutane damar shiga harabarsu suna da alhakin tabbatar babu wanda zai shiga face ya sanya takunkumin rufe fuska.

Mashawarcin gwamnan ya ce direbobin haya kada su dauki fasinjoji da suka wuce sama da mutum biyu a kowane sahu daya na kujerun ababen hawansu, yayin da aka bai wa gidajen saukar baki damar su ci gaba kasuwarsu.

Kazalika, sabuwar dokar ta ce wuraren shagulgula, mashaya, wuraren motsa jiki, wuraren casu da kuma makarantu za su ci gaba da kasancewa a rufe har sai an ga abin da hali ya yi.