COVID-19 ta kashe ma’aikatan lafiya 180,000 —WHO

WHO na bukatar samar da karin allurar rigakafin COVID-19 guda miliyan 500.

COVID-19 ta kashe ma’aikatan lafiya 180,000 —WHO

Akalla ma’aikatan lafiya 180,000 ne suka rasa rayukansu a fadin duniya sakamakon kamuwa da cutar COVID-19, kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana.

WHO ta fitar da kididdigar ce a cikin wata takarda mai taken: ‘Tasirin COVID-19 ga ma’aikatan lafiya: Adadin wadanda suka mutu’.

Takardar ta bayyana mutum miliyan 3.4 a matsayin wadanda suka mutu a dalilin cutar ta coronavirus a fadin duniya.

WHO ta bukaci samun karin hadin gwuiwa daban-daban daga masu ruwa da tsaki a fadin duniya don dakile cutar baki daya a fadin duniya.

Darakta-Janar na hukumar, Dokta Tedros Ghebreyesus, ne ya bayyana a ranar Alhamis.

“COVID-19 na da matukar tasiri da illa ga rayuwarmu, yanzu mu dubi yadda muka dogara ga wanda suke ba mu kulawa, su ma sun kasa samun kariya.

“Yana da kyau a maida hankali wajen yi wa ma’aikatan lafiya rigakafin COVID-19 don su ma su samu kariya.

“A Afirka mutum daya a cikin ma’aikatan lafiya 10 ne ke samun damar yin rigakafin cutar, wanda kuma a wasu kasashen kaso takwas cikin 10 na ma’aikatan lafiya sun yi allurar rigakafin.”

Tedros, ya ce nan ba da jimawa ba za a sake samar da karin allurar rigakafin COVID-19 guda miliyan 500.