COVID-19 ta kashe minista a Zimbabwe

Ministan Harkokin Wajen Zimbabwe, Sibusiso Moyo ya mutu ranar Laraba, kwana daya bayan ya kamu da cuta Korona.

COVID-19 ta kashe minista a Zimbabwe

Ministan Harkokin Wajen Zimbabwe, Sibusiso Moyo

Ministan Harkokin Wajen Zimbabwe, Sibusiso Moyo ya mutu ranar Laraba, kwana daya bayan ya kamu da cuta coronavirus.

Mukaddashin Babban Sakataren Shugaban Kasar kuma dan Majalisar Zartarwar kasar, George Charamba ne ya tabbatar da rasuwar a wata sanarwa.

Daya daga cikin iyalan mamacin ma ya tabbatar da rasuwar mamacin ga Kamfanin Dillancin Labaran kasar China, Xinhua.

“Gaskiya ne, dan uwana ya rasu bayan kamuwa da COVID-19 a jiya,” a cewar daya daga cikin iyalan mamacin.

Mista Sibusiso dai shi ne babban jami’in gwamnatin kasar na uku da ya rasu sakamakon cutar, tun farkon shigarta kasar a watan Maris din 2020.

Ministan, wanda tsohon soja ne, na daya daga cikin wadanda suka jagoranci juyin mulkin da ya hambarar da gwamnatin tsohon Shugaban Kasar, marigayi Robert Mugabe a watan Nuwamban 2019.

Daga bisani ne kuma Shugaban Kasar mai ci, Emmerson Mnangagwa ya nada shi a matsayin daya daga cikin ministoci a gwamnatinsa.

Boko Haram sun ƙone makarantu a Borno

Har yanzu ’yan bindiga ba su saki matar Manjo Janar Rabe ba

An binne gawar Manjo Janar Rabe a Katsina

Wasu tsiraru ne ke rura matsalar tsaro a Najeriya — Christopher Musa