COVID-19 ta kashe ministoci 2 a Malawi

A kasar Malawi, rahotanni sun tabbatar da mutuwar ministoci biyu bayan sun kamu da cutar COVID-19.

COVID-19 ta kashe ministoci 2 a Malawi

COVID-19

A kasar Malawi, rahotanni sun tabbatar da mutuwar ministoci biyu bayan sun kamu da cutar COVID-19.

Ministocin dai wadanda suka hada na Sufuri da Ayyuka, Sidik Mia da kuma takwaransa na Kananan Hukumomi, Lingson Berekanyama sun mutu ne da safiyar ranar Talata, mako daya bayan an tabbatar sun kamu da cutar.

Cutar dai ta sake barkewa a kasar bayan da akalla mutane 50 sun mutu daga ranar daya ga watan Janairun 2021.

Ko a ranar Asabar kawai sai da rahotanni suka tabbatar da rasuwar mutane 12, yayin da 10 kuma suka rasu ranar Litinin, duk a sanadiyyar cutar.

A ranar ta Litinin dai an sami karin mutum 452 da suka kamu da ita, adadin da ya haura na kowacce rana tun da ta fara bulla a watan Afrilun 2020.

Bincike dai na nuna cewa akasarin wadanda suka kamu da cutar sun dauke ta ne daga wadanda suka shiga kasar daga Afirka ta Kudu, wacce daya ce daga cikin kasashen da suka fi yawan massau cutar a Afirka.

A yanzu haka Malawi na duba yuwuwar ko dai ta bude makarantun kasar ko kuma ta rufe su a kokarin dakile yaduwar cutar.