COVID-19 ta sake kashe mutum 33 a Najeriya – NCDC

Hakan dai na nuni da cewa adadin mutanen da cutar ta kashe ya kai 2,837.

COVID-19 ta sake kashe mutum 33 a Najeriya – NCDC

Kisan COVID-19

Sabbin alkaluma daga Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Kasa (NCDC) a ranar Lahadi sun nuna cewa cutar COVID-19 ta sake hallaka mutum 33 a Najeriya, yayin da wasu 125 kuma suka kamu da ita.

Hakan dai na nuni da cewa adadin mutanen da cutar ta kashe tun bayan bullarta a kasar ya kai 2,837.

Hukumar dai a cikin alkaluman cutar da take wallafawa a kullum ta rawaito cewa ya zuwa yanzu, jimlar wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar sun kai 209,298, inda daga ciki 197,143 suka warke.

A ranar Lahadin da ta gabata dai, NCDC ta rawaito cewa karin mutum 32 da suka mutu a Legas sun kunshi adadin da aka hada tun daga ranar 11 ga watan Satumba.

Hakan dai ya sa adadin wadanda suka mutu, wanda a da bai wuce 2,769  a ranar 15 ga watan Oktoba ya tsallaka zuwa  2,804 a ranar 16 ga watan, sai kuma 2, 837 a ranar Lahadi.

Kazalika, rahoton ya nuna ana samun karuwar yawan mutanen da suke kamuwa da cutar a kulli yaumin.

A cewar NCDC, Jihohin da aka fi samun sabbin masu kamuwa da cutar a ’yan kwanakin nan sun hada da Legas da Ribas da Abiya da Anambra da Kuros Riba da kuma Edo.