COVID-19 ta mayar da ci gaban duniya baya da shekara 20 –Bill Gates
Sabon rahoton Gidauniyar Bill da Melinda Gates ya gano cewa cigaban duniya ya samu mummunar koma-baya da fiye da shekara 20 sakamakon cutar coronavirus. Rahoton ya nuna cewa fatara ta karu da kashi 7 cikin 100, yayin da bayarwa ko samar da alluran rigakafin cututtuka suka yi rikitowar da ba su taba yi ba tun […]
Sabon rahoton Gidauniyar Bill da Melinda Gates ya gano cewa cigaban duniya ya samu mummunar koma-baya da fiye da shekara 20 sakamakon cutar coronavirus.
Rahoton ya nuna cewa fatara ta karu da kashi 7 cikin 100, yayin da bayarwa ko samar da alluran rigakafin cututtuka suka yi rikitowar da ba su taba yi ba tun farkon shekarun 1990, inda matsalar tattalin arziki ke kara haifar da babban gibi a tsakankanin al’ummomi.
Attajirin duniya wanda ya kirkiro da manhajar Microsoft, Bill Gates ya fada wa sashin Ingilshi na BBC yadda cutar coronavirus ta haddasa hauhawar farashin abinci da samar da shi.
Ya kara da cewa ya “damu” kuma ya “kadu sosai” da yadda yada labaran bogi suka samu gindin zama a lokacin ganiyar cutar.
…Ya rasa mahaifinsa
A wani labarin da Aminiya ta ruwaito, Mista Bill Gates, ya rasa mahaifinsa, William Henry Gates II a ranar Litinin yana da shekara 94.
Cutar Alzheimer da ke shafar kwakalwa ce ta yi ajalinsa, kamar yadda iyalansa suka tabbatar a yayin sanar da mutuwar dattijon.
Marigayi William tsohon soja ne kuma yana cikin wadanda suka kirkiri wani kamfanin harkokin shari’a da ake kira Seattle Law Firm.
Bill Gates mai shekara 64, ya ce sun yi babban rashi kuma zai dauke su tsowon lokaci suna jimamin rasuwar mutumin da ya yi tasiri a rayuwar mutane da dama.