COVID-19 ta sake kama mutum 1,005, ta kashe 24 a Najeriya
Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Kasa (NCDC) ta ce an samu karin mutane 1,005 da suka sake harbuwa da cutar COVID-19.
Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Kasa (NCDC) ta ce an samu karin mutane 1,005 da suka sake harbuwa da cutar COVID-19.
Hukumar ta kuma ce karin wasu 24 sun mutu cikin sa’o’i 24 da suka wuce.
- Yadda ’yan bindiga suka kashe mijina wata daya da aurenmu
- Titin Kano-Maiduguri: Gwamnati ta ba da wa’adin wata 10 a kammala
NCDC ta wallafa wannan alkaluman ne a shafinta na intanet, inda ta ce ya zuwa yanzu, adadin wadanda suka kamu da cutar a kasar a yanzu ya kai 144,521.
Adadin mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon harbuwa da cutar ya kai 1,710 kamar yadda alkaluman na NCDC suka nuna.
Ta kuma ce karin mutum 1,005 sabbin harbuwa da cutar sun fito ne daga jihohi 18, ciki har da Babban Birnin Tarayya Abuja.
Jihohin da aka samu sabbin kamuwa da cutar a ranar Juma’a sun hada da Legas mai mutum 204, Kwara, 155; Oyo, 124 da kuma Jihar Filato mai mutum 80.
Abuja na da 75, sai Edo, 56; Osun, 48; Ondo, 41; Kaduna, 40; Ribas, 40; Taraba, 35; Borno, 32; Ekiti, 21; Ogun, 20; Kano, 14; Bayelsa, 8; Delta, 7; Bauchi, 3; sai Jihar Jigawa mai mutum 2.
Kazalika NCDC ta ce an sallami karin mutum 854 da suka warke daga cutar a ranar Juma’a.
Ya zuwa yanzu, Najeriya na da mutum 1,398,630 da aka yi wa gwajin cutar coronavirus tun lokacin da ta fara bulla a ranar 27 ga watan Fabrairun 2020.