COVID-19 ta sake kama mutum 880 a Najeriya — NCDC
Hukumar ta gargadi ’yan Najeriya su yi taka-tsan-tsan lokacin Sallar Layya
Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Najeriya (NCDC) ta yi gargadin cewa cutar COVID-19 ta sake dawowa Najeriya ka’in da na’in, inda ta sake kama mutum 880 cikin mako guda.
NCDC ta ce adadin mutanen sun kamu ne daga tsakanin biyu zuwa takwas ga watan Yulin 2022, kodayake ba ta kashe kowa ba a lokacin.
- Zaman lafiya zai dawo Najeriya kafin Buhari ya bar mulki — Malami
- ’Yan bindiga sun kara sakin 7 daga cikin fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna
Hakan dai na kunshe ne a cikin wasu bayanan da hukumar ta wallafa a shafinta na intanet ranar Asabar, inda ta ce Jihar Legas ce ke kan gaba a yawan wadanda suka kamu din.
Hukumar ta ce Jihar ta Legas, wacce har zuwa yanzu ita ce cibiyar cutar a Najeriya na da mutum 750 daga cikin 880 din da suka kamu.
Alkaluman dai na nufin a yanzu adadin mutanen da suka kamu da cutar ya kai 258,517, yayin da adadin wadanda suka mutu ya kai 3,144.
Hukumar ta kuma ce har yanzu akwai mutum 4,206 da ke dauke da cutar, sai kuma wasu 250,388 da suka warke kuma aka sallame su tun farkon barkewar cutar a watan Fabrairun 2020.
Sauran Jihohin da suke biye wa Legas a adadin sune Abuja mai mutum 45 da Ribas mai 40 da Delta mai mutum 11, Akwa Ibom mai 11, Kano biyar, Nasarawa hudu, sai Filato mai mutum daya.
A kan haka ne NCDC ta gargadi ’yan Najeriya da su yi taka-tsan-tsan musamman lokacin shagulgulan Sallah Babba.
Ta kuma ce a tsawon mako uku a jere, adadin masu kamuwa da cutar a kowanne mako ya karu a duk fadin duniya.